Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa labarin da ke yawo a wasu kafafen yaɗa labarai na cewa an karkatar da naira biliyan 6.5 daga baitulmalin jihar ba gaskiya ba ne.
Wannan na cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran gwamnan Kano, Sanusi Bature DawakinTofa, ya fitar a ranar Litinin, 25 ga Agusta, 2025.
A cikin sanarwar, gwamnatin ta ce rahoton da jaridar Daily Nigerian ta wallafa a ranar 22 ga Agusta, 2025, kan daraktan tsare-tsaren fwamnan Kano, Abdullahi Rogo, labari ne da aka ƙirƙira domin ɓata suna.
Gwamnati ta bayyana cewa duk wani kuɗi da ake fitarwa daga baitulmalin jihar ana yin hakan ne bisa tsarin kasafi, kuma babu wani ma’aikaci da ke da ikon sarrafa kuɗin jama’a ba tare da izini ba.
Ta kuma yi ƙarin haske cewa ofishin hulɗar gwamnatin jihar shi ke da alhakin gudanar da harkokin sufuri, masauki, tarurruka da kuma karɓar manyan baƙi ciki har da jami’an gwamnati daga Abuja da ƙasashen waje inda ake yawan buƙatar kuɗaɗe masu yawa.
Sanarwar ta jaddada cewa gwamnatin Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf za ta ci gaba da gudanar da mulki bisa gaskiya da riƙon amana, tare da bayar da damar bincike ga hukumomin da suka dace idan akwai buƙata.
Haka kuma gwamnatin ta yi kira ga jama’a da su yi hattara da labaran bogi da abokan hamayya ke yaɗawa a intanet da nufin rikita jama’a.
Sai dai ta ce tunda al’amarin yana gaban kotu, ba za ta yi ƙarin bayani ba sai dai a jira hukuncin da kotu za ta yanke.
