
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Wakilin Nijeriya Majalisar Ɗinkin Duniya, Farfesa Ibrahim Gambari ya ce sama da ƙungiyoyin ƴan ta’adda guda 1,000 ne suke gudanar da ayyukansu a sassa daban-daban na Nahiyar Afirka.
Gambari, wanda shi ne shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa a zamanin marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana haka ne a babban taron jagororin tsaro na Afirka a Abuja, ranar Litinin.
Ya ce, ayyukan bincike a Nijeriya sun tabbatar da cewa akwai sama da ƴan ta’adda 1,000 a nahiyar, wanda har zuwa yanzu adadinsu ke cigaba da ƙaruwa.
Farfesan ya bayyana cewa, da dama daga hukumomin tattali na shiyyoyi suna fuskantar tsaiko dafa ayyukan ƴan bindiga da wasu nau’ukan ta’addanci a sassan ƙasashen Afirka.
Akan haka ya kirayi ƙasashen da su fara daƙile matsalolin ta’addanci a acikin al’ummunsu kafin zuea matakin shiyyoyi ko nahiya, yana mai cewa ya zama wajibi su ƙarfafa hukumomin tsaronsu da fasaharsu ta cikin gida domin kawo ƙarshen ta’addanci.
Kazalika, ya kuma nemi ƙasashen da su samar da tsarin gudanar da harkar tsaro na bai-ɗaya domin ɗorewar tsaro ga al’umma da sassansu.
