
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya koka game da gocewar jirgin ƙasa da ya ɗebo fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Talata, lamarin da ya yi sanadin raunata mutane guda shida da tilasta wa Hukumar Kula da Jiragen ƙasa (NRC) dakatar da ayyuka a hanyar.
A shafinsa na kafar X, Shugaba Tinubu duk da cewa yanzu yana ƙasar Brazil a wata ziyarar aiki, ya ce ya samu rahoton tsaikon da aka samu a ranar.
“Ina bakin ciki da wannan al’amari. Ina addu’ar jimami ga waɗanda suka jikkata, iyalansu, da dukkan fasinjojin da abin ƙuncin ya rutsa da su”, inji Tinubu.
Akan haka ne Shugaban Ƙasar ya umarci NRC da ta ɗauki matakin gaggawa wajen kauce wa sake samun faruwar irin haka a nan gaba.
Bayan faruwar al’amarin ne jim-kaɗan da tashin jirgin daga Abuja a safiyar Talata, NRC ta sanar da dakatar da aiki a ɓangaren har zuwa lokacin da za ta kammala bincike a kai.
Hukumar ta kuma yi watsi da jita-jitar cewa rashin kula da jiragen yadda ya dace ne sababin aukuwar hatsarin.
