Gwamnatin Katsina za ta yi bincike kan tamowa a jihar

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina za ta gudanar bincike na musamman domin gano yadda matsalar rashin abinci mai gina jiki (Tamowa) ke shafar al’umma a faɗin jihar.

Lokacin da yake ƙaddamar da kwamitin binciken, muƙaddashin gwamnan jihar, Honorabul Faruq Lawal Jobe wanda ya samu wakilcin kwamishinan harkokin ƙananan hukumomi da masarautu, Alhaji Tanimu Dutsinma ya bayyana cewar, manufar binciken shi ne tantance al’ummomin da ke fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki, nazartar raunin ƙarfin iyali ga cimaka mai gina jiki, da kuma ƙayyade matsakaicin kuɗin da ake kashewa a gida don abinci.

Ya ce, gwamnatin jihar ta ɗauki matakai na dogon lokaci wajen tsaron abinci, ciki har da: Siyan manyan taraktoci 400 domin inganta noma, samar da taki mai rangwame ga manoma, da ninka tallafin kuɗaɗe ga harkar noma daga Naira Miliyan 200 a shekarar 2023, zuwa Naira Miliya 250 a shekarar 2024 da kuma linka su zuwa Miliyan 500 a shekarar 2025, yana mai cewar,”inji Joɓe

Tun zuwan wannan gwamnatin ake ci gaba da samar da taki mai rangwame ga manoma don samun amfanin gona mai yawa.”

A cewar Jobe, wannan bincike da za a aiwatar zai ba gwamnatin damar ƙara bibiyar ci gaban ayyuka da tantance tasirinsu, domin tabbatar da ƙoƙarin da gwamnati ke yi ya yi tasiri.

A nasa jawabin, shugaban kwamitin, Sheikh Ahmad Filin-Samji, ya bayyana cewar binciken da kwamitin zai yi zai ratsa gidaje 8,500 a faɗin jihar, tare da horas da kusan ma’aikata 200 domin tattara bayanai bisa ƙa’idar duniya.

Sheikh Ahmad ya kuma yi kira ga ma’aikatan da za a horasa da su ɗauki aikin a matsayin ibada, tare da sadaukar da kansu domin ci gaban al’umma.

Farfesa Saifullahi Sani, babban jami’in shima a wajen taron ya bayyana cewa tattara sahihan bayanan da za a yi zai taimaka sosai wajen samar da tsare-tsaren rigakafi da kariya kan yunwa da rashin abinci mai gina jiki, domin a magance matsalar tun kafin ta tsananta

By ukarofi