Ba ma ɗaukar sababbin ma’aikata, shafin bogi ake yaɗawa – NECO

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Gudanar da Jarrabawa ta Ƙasa (NECO) ta yi watsi da rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa tana ɗaukar sabbin ma’aikata, inda ta bayyana hakan a matsayin ƙarya mara tushe da ake amfani da shi wajen yaudarar al’umma.

A wata takarda da Daraktan yaɗa labaranta, Azeez Sani ya fitar a ranar Laraba, NECO ta ce ba ta fara ɗaukar ma’aikata ba, kamar yadda ba ta da shirin haka a nan kusa.

Ta bayyana cewa saƙon da ake yaɗawa abu ne daga ƴan damfara da ke neman cutar da duk wanda ya faɗa wa tarkonsu.

Don haka ta shawarci ƴan Nijeriya da su yi watsi da shi, tana mai gargaɗinsu da cewa wasu ƴan damfara ne suke ƙoƙarin damfarar masu neman aiki ruwa-a-jallo ta hanyar amfani da shafukan ƙarya.

Kazalika, ta ce za ta sanar da fara ɗaukar aiki ne bayan gwamnatin tarayya ta amince da hakan tare da bin matakan da suka dace.

By Babaji