Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa ya kai ziyarar jajantawa a ƙauyen Mantau da ke ƙaramar hukumar Malumfashi inda ya jajantawa iyalan waɗanda harin ‘yan bindiga ya shafa a wani masallaci.
Gwamna Raɗɗa, ya katse hutun jinya da yake yi a ƙasar waje domin dawo wa gida don jajantawa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, gwamnan ya sanar da bayar da tallafi na Naira dubu 500,000 ga kowane gida.
Da yake jawabi ga iyalan da suka rasa rayukan ‘yan uwansu gwamnan ya bayyana cewa, “Duk irin damuwar da kuka shiga sakamakon wannan hari, ina jin shi a cikin zuciyata, ni ma na rasa ɗan uwa a wannan matsala ta rashin tsaro, shi ya sa nake tabbatar muku da cewa gwamnatin nan za ta ci gaba da ɗaukar ƙwararan matakai na maido da zaman lafiya.”
Raɗɗa ya kuma umurci shugaban ƙaramar hukumar Malumfashi da ya haɗa kai da sarakunan gargajiya wajen tara matasa da horar da su domin kare al’ummar yankin, ya kuma bayar da tabbaci ga mazauna yankin na ci gaba da ƙoƙarin kafa sansanin soji a shiyyar Malumfashi.
Gwamna Raɗɗa ya kuma yi alƙawarin gina makaranta da asibiti na zamani, da gyaran masallacin da ‘yan bindigar suka lalata, da gina hanyoyin shiga ƙauyen domin ba da damar kai ɗauki ga jami’an tsaro idan buƙatar hakan ta taso.

“Gwamnatin jiha za ta gyara duk gidajen da waɗannan masu laifin suka lalata,” In ji shi.
Gwamnan ya kuma yi kakkausan gargaɗi ga masu amfani da matsalar rashin tsaro domin cimma wata manufa ta siyasa.
“Tsaro shi ne ceto rayukan al’umma ba siyasantar da shi ba, duk wanda ya tada zaune tsaye za mu yi maganinsa, kuma In Sha Allahu za mu yi nasara a kan haka.”
Da yake jawabi yayin ziyarar, Hakimin Malumfashi, Mai Shari’a Sadiq Abdullahi Mahuta (rtd), ya yaba da jajircewar Gwamnan wajen yaƙi da rashin tsaro.
