Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina ya faɗi haka yayin da yaje ta’aziya a ƙauyen Gidan Mantau da ke ƙaramar hukumar Malumfashi.
Haka kuma yayi alƙawarin gyara masallacin da ƴan bindigan suka lalata.
Ƙauyen Mantau ne inda ƴan bindiga suka kashe mutane fiye da 50 a yayin da suke gudanar da Sallar fijr a wani masallaci da ke cikin ƙauyen.
Kafin wannan ziyarar ta Dikko Raɗɗa,sai da muƙaddashin Gwamnan jihar Farouk Lawal Joɓe tare da manyan jami’an tsaro na jihar suka kai ziyarar ta’aziya ga iyalan mutanen da ƴan bindiga suka kashe.
Gwamnan wanda ya katse hutun da yake domin duba lafiyar sa a ƙasar waje ya gudanar da wata muhimmiyar ganawa ta musamman da dukkan ƴan majalisar dokokin tarayya da na jihar guda a gidan gwamnatin jihar da ke garin Abuja da Kaduna.
Ganawar, wacce ta gudana a cikin yanayi na sirri da natsuwa, ta mayar da hankali ne kan irin ƙalubalen tsaro da jihar Katsina ke fuskanta a halin yanzu. An tattauna hanyoyi daban-daban da za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin jihar, tare da lalubo sabbin dabarun da za su kawo sauƙi ga jama’a.
Gwamna ya bayyana cewa gwamnatin sa ta ɗauki batun tsaro a matsayin ginshiƙin duk wani ci gaba, domin babu ci gaban tattalin arziki ko jin daɗin al’umma idan babu kwanciyar hankali. Ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin ɓangaren zartarwa da na dokoki wajen fitar da tsare-tsaren da za su magance matsalar tsaro ta fuska daban-daban.
Ƴan majalisar dokokin sun nuna goyon baya da ƙudurin yin aiki tare da gwamnatin jihar domin ganin an cimma wannan buri na samar da tsaro ga kowa da kowa.
Haka kuma sun yabawa Gwamna Raɗɗa bisa jajircewarsa da irin namijin ƙoƙarin da yake yi tun bayan hawansa mulki, wajen fuskantar matsalolin da suka daɗe suna damun al’ummar Katsina.
Bayan ganawar ɓangaren gwamnati, ƴan majalisar sun amince da haɗa kai wajen aiwatar da matakan gaggawa da kuma dogon lokaci, waɗanda za su zama mafita ga matsalar tsaro a Jihar Katsina.
