Janar Sani Sami: Badakkare mai dakawa Tatsine kashi

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Haƙiƙa labarin rasuwar mai martaba Sarkin Zuru Goma II Janar Muhammadu Sani Sami ya kawo juyayi da tuna barden soja da gadon sarauta ya sa ya yi shiru ya takaita kansa ga lamuran jagorantar jama’a daga masarautar Zuru a jihar Kebbi arewa maso yammacin Nijeriya. Matasa na zamanin yau ba su ma san lokacin da marigayin ya yi aikin soja ba musamman da irin rawar da ya taka na yaƙi da ‘yan maitatsine da ke zaman wasu ‘yan ta’adda masu yanka mutane haka siddan kamar yankan rago. Don haka ‘yan Boko Haram da su ka fito fili a wajajen 2009 da yanka mutane ba su zama farau ga wannan ta’addancin ba hatta a Maiduguri babban birnin jihar Borno don ‘yan maitatsine sun yanka mutane. An samu ta’addancin ‘yan maitatsine a kano inda nan ne a ka kashe jagoran tafiyar Muhammadu Marwa. Illar ta shiga Maiduguri, Gombe da kuma Yola a jihar Adamawa. Mun wayi gari a Lahadin da ta gabata da labarin Allah ya yi wa mai martaba Sarkin Zuru Manjo Janar Sani Sami rasuwa bayan fama da jinya a wani asibiti a London.

Manjo Janar Sani Sami wanda ya yi aikin soja gabanin zama Sarki ya zama kantoman soja na jihar Bauchi lokacin mulkin soja na marigayi Janar Muhammadu Buhari.

Haƙiƙa jihar Bauchi ta samu kantomomin soja biyu daga jihar Kebbi da su ka haɗa da marigayi Kanar Bello Kaliel a 1976 sai Manjo Janar Sani Sami 1984.

Tuni a ka fara miƙa saƙon ta’aziyya bisa wannan rashi na Sarkin Zuru.

Da ganin rasuwar Janar Sani Sami sai tarihin yanda yakin ‘yan maitatsine ya auku a Gombe cikin tsohuwar jihar Bauchi ya fado min. Marigayii Janar Sani Sami na kujerar kantoman soja na jihar Bauchi kuma bai yi kasa a gwiwa ba ya taho Gombe da ke kimanin nisan kilomiya 155 daga Bauchi don tinkarar ‘yan maitatsine da kan shiga gida-gida su na yanka mutanen da ba sa kan tafiya ɗaya da su wato bin addinin gardawa masu ganin duk hadisan Manzon Allah a matsayin wani kato ne ya ruwaito su don haka a ke mu su laƙabi da ‘yan kala kato amma don yadda su ke cewa “Allah ta tsine” da hakan ruwaya ta zo ya fito daga bakin Marwa Maitatsine don yanayin gwarancin Hausar sa sai su ka shahara da zama ‘yan maitsine wato mutane da kan tsinewa duk masu bin sunnar Manzon Allah don su a wajen su Alkur’ani mai girma kaɗai ne za a yi aiki da shi ba batun hadisi. Kazalika in ma da za su fahimci Alkur’anin su yi aiki da shi to ba shakka a karshe ba za su riƙa tsinewa wadanda ba sa bin hanyar su ko ma ya kai ga yi mu su yankan rago ba. Gardawa da kan karanta Alkur’ani ba tare da sanin fassarar sa ba, ai ba zai yiwu a ce za su fahimci koyarwar Manzon Allah ba. Marigayi Janar Sani Sami ya zo ya tabbatar an ɗau matakai da za su kare jama’a duk da tuni ma ‘yan ta’addan sun riga sun yanka mutane da dama gaske. A ido na mutane su ka riƙa ficewa daga cikin garin Gombe su na hijira zuwa wasu yankunan karamar hukumar Akko don tsira da ran su. Waɗannan gardawa da su ka kafa tunga a wata anguwa yanzu da a ke kira Malam Kuri wajen mangorori a Gombe sun dukufa ga karatun Alkur’ani da yi ma sa fassarar gatari. Kafin su aiwatar da zubar da jini mutane kan ziyarce su har ma su yi hulɗa da su tamkar dai bakin malamai masu kaunar karatun tsangaya na allo. Kwamandan rundunar tatsine ta Gombe Musa Makaniki ya zauna a anguwar Jekadafari da ke tsakiyar Gombe don haka duk fafatwar da a ka yi ba ta shafi anguwar ba. Wadanda su ka cije da dama sun zauna a anguwar ba su yi gudun hijira ba ciki kuwa har da ni mai rubutun nan Nasiru Adamu El-hikaya da marigayi mahaifina Alhaji Adamu Miagoro da sauran ‘yan gidan mu. Mun zauna a gida mu na jin karar rugugin musayar harbin bindigogi tsakanin ‘yan maitatsine da jami’an tsaro. Ta hanyar kallon akwatin talabijin a NTA mu ke ganin abubuwan da su ke faruwa na matakan marigayi Janar Sani Sami Badakkare mai dakawa ‘yan tatsine kashi.

‘Yan maitatsine sun yi kundunbala ma a wani lokacin har su ka kwace motar ‘yan sanda da bindigogin jami’an tsaro. Wato abun da ke faruwa shi ne kwamandan ‘yan ta’addan kan ba da umurnin a kwato ma sa motar ‘yan sanda ko duk abun da ya ke buƙata. ‘Yan maitatsine kan nufi duk inda a ka tura su ba fargaba har su cimma burin su. A shekarun 1980 ba a san tashin hankali na zubar da jini a cikin gari kamar na maitatsine ba. Mun samu tabbacin ‘yan ta’addan kan shiga gidaje su yanka maza su bar mata. Su kan tari jinin wadanda su ka yanka a kwanon sha su kwankwade don hakan kan sa zuciyar su ta bushe ya zama ba sa ko gezau ga ta’addancin da su ke yi. A unguwar Herwagana a ka fi samun yawan zubar da jini inda a ka yi musayar wuta kuma har ‘yan wasu shekaru 20 haka da su ka wuce akwai wasu gidaje da ke da shaidar dukan albarusai a Herwagana kan titin zuwa sabuwar kasuwa da wajajen gidan wani ɗan kasuwa Alhaji Saurayi. Musa Makaniki ya jagoranci zaratan jami’an zubar da jini na maitatsine su ka dau fagen yaƙi a tudun hatsi na Gombe da a ke kiri Tudun Hatsi inda a ke tara kayan abinci a dubban buhuna a tura duk sassan kasar nan musamman kudancin Nijeriya. Na kwan biyu ban leka kasuwar ba amma ina ganin har yanzu a kan yi harkar kasuwancin buhunan hatsin. Bigiren na nan gefe kaɗan ta tsallaken titi da babban ofishin ‘yan sanda na cikin garin Gombe. Ko lokacin da ‘yan Boko Haram su ka kai hari Gombe a zamanin tsohon gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo, wannan ofishin su ka tunkara. Kwamanda Musa Makaniki ya cije a ka yi ta musayar wuta tsakanin jama’ar sa da ‘yan sanda har lokacin da fitinar ta lafa. Ina ganin wasu ‘yan maitsatsine a lokacin sun yi hijira ne zuwa wasu garuruwa har harkar ta kala kato ta samu cikas ɗin zama marar hujja da mabiya. ‘Yan maitatsine kan kashe Musulmi da ma wanda ba Musulmi ba. Wato ma’ana su kan yanka duk wanda ba gardi dan ƙungiyar su ba kamar yadda ‘yan Boko Haram su ke yi. Zan tuna babban Fasto na majami’ar Baptist da ke nan anguwar Jekadafari ya gamu da ajali lokacin da ya ke tafiya anguwa ko dawowa daga Herwagana kan magamar hanyar da a ke kira Inna Lillahi don yadda a kan samu hatsarin masu Babura a titin da a ke kira da Titin Bello Sabon Kuɗi. ‘Yan maitatsine sun kashe Faston kuma in zan tuna sosai ya na cikin motar nan ne da a ke kira gilma wato fijo STATION WAGON. Yanzu haka kabarin sa na nan a danger yammacin majami’ar ta can kuryar arewa da a can baya ke iyaka da gonar makarantar firamare ta Jekadafari da tsohuwar makarantar sakandanren gwamnati GSS Gombe. Bayan kura ta lafa mu kan je bigiren a lokacin mu na yara ‘yan firamare kuma tun daga nan lamuran tarihi su ke daukar hankali na. Zan zaiyana Gombe da zama fagen yaƙi na ƙarshe na gamawa da ‘yan ta’addan kala kato masu shan jini kuma sunan marigayi Janar Sani Sami ba zai gushe a tarihi kan yaki da ‘yan mai tatsine ba. Daga bisani an jbge ‘yan sandan kwantar da tarzoma a Gombe da kan tilastawa mutane su buɗe cikin su daidai cibiyar su don jin labarin ‘yan mai tatsine na da wata shaida da a kan gane su da ita. Idan mutum ya zo wucewa a kan umurce shi ya daga hannun sa sama in ya iso ya buɗe cunar rigar sa a duba don tantance shin ya na cikin mayakan gardawa ne ko kuwa a’a. A ido na a ka tafi da wani malamin allo a nan unguwar Jekadafri da a ka gano ya na cikin maitatsine. Gaskiya ban san matakin da a ka ɗauka a kan sa ba amma ko banza zaman irin su a wannan anguwa da ke tsakiyar garin Gombe ya sa ba a harba ko albarushi daya a cikin ta ba. A nan tsohuwar maƙabartar Gombe da ken an anguwar ta Jekadafri a ka bunne akasarin waɗanda ‘yan maitatsine su ka yanka. Ba mamaki wasu marigayan ya zama su na hurumin Da’u da ke kudancin gari. Duk wanda bai ga tashin hankalin mai tatsine ba da sauran sa wajen tarihin yanda mutanen da ba a yi tsammani ba kan juye daga sunan gardawa masu karatu zuwa gaggan ‘yan ta’adda masu shan jini.

KAMMALAWA

Ba zan kammala wannan rubutu ba tare da miƙa saƙon ta’aziyya ta ga al’ummar tsohuwar jihar Bauchi da kuma jihar Kebbi ta yanzu musamman Masarautar Zuru bisa rasuwar babban Badakkare Janar Sani Sami da a ka gwabzan yaƙin ƙarshe da shi na murƙushe masu kisan gilla ga waɗanda ba su yi mu su laifin komai ba sai ko a ce yarda da sahihancin hadisan Manzon Allah mai tsira da aminci!

By ukarofi