Daga IBRAHIM HAMISU Kano
Ƙungiyar ’yan jarida ta Bichi, wato Bichi Journalists Forum ƙarƙashin jagorancin Alhaji Musa Yahaya Bichi, ta kai ziyarar ban girma ga shugaban ƙaramar hukumar Bichi na Jihar Kano, Hon. Hamza Sule Maifata, a ranar Laraba.
A yayin ziyarar, shugaban ƙungiyar ya yaba da jajircewar Hon. Maifata wajen aiwatar da ayyukan ci gaban ɗan Adam da kuma na gine-gine a faɗin ƙaramar hukumar. Ya jinjina masa musamman ga damar tallafin karatu da aka bai wa ɗimbin matasa a Bichi, tare da yabawa haɗin gwiwar da ke tsakanin Hon. Maifata da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Bichi, Hon. Abubakar Kabir Abubakar. Ya bayyana wannan haɗin gwiwar a matsayin “Siyasar ci gaba” wadda ke sauya Bichi zuwa ƙaramar hukuma abin koyi.
Ƙungiyar ta kuma shawarci shugaban ƙaramar hukuma da ta dawo da tsarin sanya lambar gidaje, tana mai cewa wannan zai taimaka wajen ƙara tsaro, tare da kiyaye tarihin gari da kuma fitattun mutane da suka taka rawa a cikin al’umma.
Kazalika, Alhaji Musa Yahaya Bichi ya buƙaci kafa kwamitin kula da samar da ayyukan yi ga matasa, domin tabbatar da rabon ayyuka cikin adalci da kuma faɗaɗa damar samun aiki ga matasan Bichi.
A nasa jawabin, Hon. Hamza Sule Maifata ya gode wa ƙungiyar bisa hangen nesa da shawarwarin da ta bayar. Ya tabbatar musu cewa gwamnatinsa a buɗe take wajen karɓar muhimman shawarwari da da tsare-tsare da za su kawo ci gaba mai ɗorewa a ƙaramar hukumar Bichi, da jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.
Ziyarar ta samu halartar shugabannin ƙungiyar wanda ƴan asalin Ƙaramar hukumar Bichi ne da suka fito daga kafafen yaɗa labarai Kamar ARTV da AIT da Blueprint Newspapers da Granty Radiyo da Express Radiyo da Aminci Radiyo da Radiyo Kano da sauransu.
