‘Yan sanda za su daina gadin manyan mutane – Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirinta na kawo ƙarshen amfani da ƴan sanda da jami’an wasu hukumomi wajen gadin manyan mutane, inda ta ce ba za a cigaba da amfani da su ba wajen bada tsaro ga iya masu hali a madadin baki ɗaya al’umma.

Mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara akan tsare-tsare kuma Shugabar Cibiyar Kula da Sauke Nauyin hukumomin gwamnati, Hadiza Bala-Usman ta bayyana hakan a Abuja, ranar Alhamis.

Da take magana a taron nazarin ayyukan cikin gida, Hadiza Bala-Usman ta koka game da yadda aka karkatar da ayyukan jami’an ƴan sanda da na wasu hukumomi daga haƙiƙanin ayyukan da suka rataya da wuyansu.

A madadin haka sai suke yin hidima ga ƴan siyasa da masu kuɗi a matsayin masu gadin rayuka da dukiyoyinsu.

“Ɗaya daga cikin abubuwan da ke damuna shine idan na ga VIPs sun je wani waje sai ka ga ƴan sanda masu yawa suna kewaye da su, yayin da wasu wurare da ke buƙatar tsaro aka yi watsi da su.”

Ta bayyana cewa, gwamnati tana aiki da kamfanonin masu gadi domin ganin ta samar musu da lasisin aiki ta yadda za su karɓe baki ɗaya aikin gadin manyan mutane.

Kazalika, ta ce ta gano cewa an sauya ayyukan jami’an yaƙi da ta’addanci zuwa yi wa manyan mutane gadi, lamarin da a cewarta ya sa suka ɗauki matakan shawo kan matsalar da haɗin-gwiwar Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida.

By Babaji