Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi
Gwamnatin jihar Kebbi ta ƙaddamar da kwamiti don soma shirye-shiryen yadda za a gudanar da bikin kamun kifin ƙasa da ƙasa na Argungu da za yi a watan Fabrairu na shekarar 2026.
Babban daraktan gudanarwa na bikin Alhaji Sufyanu Garba Bena ne bayyana haka a garin Birnin Kebbi ranar Talatar da ta gabata.
Ya bayyana cewa tuni Gwamna Malam Nasir Idris ya umarci babban kwamitin shirye-shiren bikin ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar Sanata Umar Abubakar Argungu (Tafidan Kabi) da ya gaggauta kammala duk wani shiri da ya dace don ganin bikin na shekarar 2026 ya yi armashi.
Ya ƙara da cewa bayan ƙaddamar da kwamitin a shekarar 2024 bikin bai yiyu ba shekarar 2025 ba saboda waɗansu dalilai don haka aka mayar da shi zuwa shekarar 2026. Wanda in sha Allahu ana sa ran samun nasarar aiwatar da shi.
Yanzu haka dai an sake bibiyar kasafin da kwamitin ya kawo na kimanin Naira biliyan bakwai da miliyan ɗari takwas (7.8) inda aka mayar da shi biliyan uku da miliyan dari takwas (3.8).
Bena ya bayyana cewa wannan bikin na shekarar 2026 zai zama na musamman saboda akwai hanyoyi da za a ɓullo don haɓɓaka al’adun gargajiya da kuma ƙarin hanyoyin samun kuɗin shiga, saboda haka kwamitin zai cigaba da aiki ba dare ba rana har sai an kammala duk wani shiri kafin lokacin.
