Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A wani yunƙuri na bunƙasa masana’antun Nijeriya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da dokar hana fitar da ƙwallon kaɗanya wanda ake sarrafawa wajen samar da man kaɗe har na tsawon watanni shida.
Umurnin, wanda zai fara aiki nan take ya biyo bayan rahotannin tafka asara da Nijeriya ke yi sakamakon ficewa da ɗanyar kaɗanyar kafin sarrafawa, yin hakan a cewar gwamnatin zai daƙile kasuwanci mara riba da kƙarfafa masana’antun cikin gida.
Mataimakin shugaban ƙasar, Kashim Shettima, wanda ya sanar da dakatarwar a yayin wani taron masu ruwa da tsaki, ya bayyana cewa matakin zai ƙara darajta kasuwancin man kaɗe ta hanyar farfaɗo da masana’antun sarrafa kayan gida, ta yadda za su samar da ayyukan yi da ƙarin kuɗaɗen shiga ga mazauna karkara musamman mata.
Shettima ya yi hasashen cewa sake tsara kasuwancin kaɗanya zai taimaka wajen samar da ribar kusan Dala miliyan 300 a duk shekara.
Duk da cewa Nijeriya ce kan gaba wajen noman kaɗanya a duniya, a halin yanzu ba ta mallakin fiye da kashi ɗaya daga ribar dala biliyan 6.5 da Kwallon ke samarwa a kasuwannin duniya.
A cewar ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari, an kiyasta cewa Nijeriya na asarar kimanin tan dubu 90 na ɗanyen man kaɗanya a duk shekara sakamakon rashin bin ƙa’idojin cinikayya na bai ɗaya.
Ana sa ran matakin da zai biyo bayan dakatarwar zai taka rawa waken rage dogaron da Najeriya ke yi da man fetur wajen samar da kudaden shiga
Tuni ƙasashe masu maƙwabtaka da Nijeriya da suka haɗa da Ghana, Burkina Faso, Mali, da Togo suka ɗauki irin wannan mataki don farfaɗo da kasuwancin ƙwallon ƙadanya a ƙasashen su.
