
Gwamna Uba Sani bai taɓa zama abokina ba, inji El-Rufa’i
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya bayyana cewa gwamnan jihar na yanzu, wato Uba Sani ba abokinsa ba ne.
El-Rufa’i mai shekaru 65, ya bayyana haka ne a ranar Lahadi yayin hira da gidan talabijin na Channels.
Haka kuma, ya ƙaryata batun da ake yaɗawa cewa akwai takun-saƙa tsakaninsa da gwamnan duba da yadda ya ke sukar tsare-tsaren gwamnatin tarayya da ta jihar.
Tsohon ministan na Abuja ya ce sam babu abota tsakaninsa da gwamnan, saidai ya Uba Sani ya kasance yaronsa ne a siyasa, kamar yadda ya bayyana a hirar.
“Abinda na ke alfahari da shi shine na zame wa mutane da dama jigo ta yadda suka cigaba a rayuwa, wasu ma har sun fi ni, kuma ina alfahari da hakan”, inji shi.
El-Rufa’i ya kuma zargi Uba Sani da hannu a harin da aka kai wa taron ADC na ƙaddamar da kwamiti a Kaduna ranar Asabar da ma akan wasu ƴan siyasa a jihar.
