Ƙungiyar Kansilolin APC ta jinjina wa Gwamnan Kebbi kan biyan tsofaffin kansiloli haƙƙinsu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar kansilolin jam’iyyar APC ta ƙara NPCF, ta yaba wa Gwamnan Kebbi, Dr. Nasir Idris Ƙauran Gwandu bisa karamcinsa na sahale wasu maƙudan kuɗaɗe da adadinsu ya kai biliyan N2.185 don kammala biyan dukkanin bashin da tsoffin kansilolin jihar tun daga zangon 2004 zuwa 2024 suke bin gwamnati.

Ta bayyana shi a matsayin shugaba mai tsananin tausayi bisa share kukan waɗannan bayin Allah game da haƙƙoƙinsu na tsawon sama da shekaru 20.

Hon Muslihu Yusuf Ali, a wata takarda, ya kuma taya ƴan jihar kebbi murnar manyan ayyukan alheri da na more rayuwa da farfaɗo da ƙananan hukumomi da walwalarsu kamar yadda shugaban kasa Bola Tinubu ya ƙudiri aniyar yi daga kuɗaɗen shirin RENEWED HOPE domin jin dadin kowanne ɗan ƙasa.

An yi wannan bayani ne a lokacin da shugaban kansilolin APC’n kasa Muslihu Yusuf Ali ya ziyarci jihar bisa ganawa ta musamman tare da shugabancin zaɓaɓɓun kansilolin jihar a karkashin jagorancin Hon Abba Ɗan sabo shugaban kasilolin jihar kebbi, ranar 2/9/25 a dakin taro na shagalinku hotel dake T/wada cikin Birnin kebbi, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

By Babaji