Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina malam Dikko Raɗɗa ya amince da naɗa Tasi’u Dahiru PHD da Aminu Lawal Jibiya a matsayin masu bashi shawara kan ilimin almajiranci da na cigaban al’umma.
Babban jami’in yaɗa labarai na gwamnan Muhammad kaula ya fitar da wannan sanarwa da aka rabawa manema labarai a Katsina.
Tasi’u Dahiru wanda tsohon kwamishinan ayyuka ƙarƙashin gwamna Aminu Masari shine zai kasance mai ba gwamna shawara kan ilimin almajiranci da yaran da basa zuwa makaranta.
Aminu Lawal Jibiya shine mai ba gwamna shawara kan cigaban al’umma,kafin nan ya taɓa riƙe muƙamin mai baiwa gwamna shawara kan ƙwadago ya kuma riƙe muƙamin zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar Jibiya.
Shine Alhaji Tasi’u Dahiru wanda ya taɓa riƙe muƙamin kwamishinan ayyuka da gidaje a gwamnatin Rt Hon Aminu Bello Masari ya kuma taɓa zama shugaban ƙaramar hukumar Ɓatagarawa.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya taya su samun muƙamin na masu bashi shawara tare da fatan za su yi amfani da ƙwarewar su wajen taimakawa ƙudirin gwamnatin Dikko Raɗɗa na (Building Your Fure) watau gina cigaban al’umma.
