Hedikwatar tsaro ta bayyana ta’adin da ta yi wa ’yan ta’adda a watan Agusta

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hedikwatar tsaro (DHQ) ta sanar da samun gagarumar nasara a yaƙin da ake yi da ta’addanci, ‘yan fashi da sauran matsalolin tsaro a faɗin Nijeriya, inda ta bayyana cewa sojoji sun kashe ‘yan ta’adda da dama, tare da cafke mutane 85 da ake zargi, tare da ceto mutane 66 da aka yi garkuwa da su a cikin watan Agusta.

Daraktan yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja, yayin da yake zantawa da manema labarai kan bitar ayyukan rundunar na wata-wata.

Dakarun Operation Haɗin Kai sun zafafa kai hare-haren ta’addanci a kan mayaƙan Boko Haram da mayaƙan IS na yankin yammacin Afirka (ISWAP). A cewar Kangye, sojojin sun kawar da masu tada ƙayar baya da dama, tare da kama mutane 15 da ake zargi da haɗa baki 13, da ‘yan bindiga, da dillalan miyagun ƙwayoyi tare da kuɓutar da wasu mutane takwas da aka yi garkuwa da su.

A Jihohin Zamfara, Sokoto, Kaduna, Kebbi, da Katsina, sojoji sun kashe ‘yan ta’adda da dama a wani samame da aka yi musu, sun kama mutane 23 da ake zargi, tare da ceto mutane 24 da aka yi garkuwa da su.

Dakarun ‘Operation Enduring Peace’ sun kashe ‘yan ta’addan, sun kama wasu masu laifi bakwai, tare da kuɓutar da wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su. Musamman ma, an kama wani mutum da ake zargi a ƙaramar hukumar Bassa da kuɗin fansa miliyan N3 da aka tanadar wa ‘yan ta’adda.

A ƙarƙashin Operation Whirl Stroke, sojojin sun kama wasu masu tsattsauran ra’ayi guda tara tare da kuɓutar da mutane 13 da aka yi garkuwa da su a yayin gudanar da aikin share fage.

Kangye ya ce sojojin na haɗin gwiwa sun kuma ƙwato manyan tarin makamai, alburusai, bama-bamai, babura, da ababen hawa daga hannun ‘yan ta’adda.

“A cikin watan da ake nazari, sojojin sun ci gaba da ƙarfafa ayyukan haɗin gwiwa da nufin kawar da barazana ga tsaron ƙasa, maido da kwanciyar hankali, da kuma kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa,” inji shi.

Sabbin sauye-sauyen na zuwa ne jim kaɗan bayan DHƙ ya bayyana cewa an kashe ‘yan ta’adda 6,260 tare da kama masu aikata laifuka 14,138 a hare-haren haɗin gwiwa na sojojin ƙasar a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Mataimakin daraktan yaɗa labarai na tsaro, Birgediya Janar Ibrahim Abu-Mawashi, ya bayyana hakan ne a farkon makon da ya gabata yayin da yake gabatar da bayyani kan nasarorin da aka samu a wani taron manema labarai da aka faɗaɗa a Abuja.

By ukarofi