Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin sayar da kamfanoni 91 mallakinta a wani sabon yunƙuri na ƙarfafa tattalin arzikin Nijeriya, da samar da ƙarin kuɗaɗen shiga, da samar da ayyukan yi.
Darakta Janar na Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamnati (BPE), Ayodeji A. Gbeleyi, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata, inda ya jaddada cewa sabon salon sayar da kamfanoni na da nufin tabbatar da ingantaccen aiki da kuma sake fasalin muhimman sassan tattalin arzikin ƙasar.
A cikin waɗanda aka lissafa akwai – Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki guda biyu (DisCos) da kuma kamfanin samar da wutar lantarki guda ɗaya (GenCo) don bayar da tallafin farko (IPOs) a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Nijeriya, duk da cewa an ɓoye sunayen sauran.
“A wannan mataki, saboda sirrin ciniki, ba mu da ikon bayyana biyu daga cikin kamfanin DisCos 11. Har ila yau, ba za mu iya bayyana GenCo da ake nufi da sirri ba kuma don kauce wa haifar da damuwa ko a tsakanin ma’aikata ko kuma sauran jama’a,” inji Gbeleyi.
Shugaban na BPE ya bayyana cewa masana’antar samar da wutar lantarki a Nijeriya na ci gaba da fuskantar cikas. Ko da yake an haɗa tasoshin wutar lantarki guda 23 da na ƙasa, kusan biyar na iya daina aiki a kowane lokaci saboda ƙarancin iskar gas, ɓarna, ƙarancin lanatarki, da kuma matsalar kuɗi.
Ya kuma ƙara da cewa, an ɗage shirin mayar da kamfanin GenCos guda biyar zuwa wani kamfani, bisa la’akari da rashin sauyi a kasuwar canji.
“Lokacin da aka fara ciniki a shekarar 2021, farashin canji a hukumance ya kai N450. A shekarar da ta gabata, ya kai Naira 1,600, kuma a yau ya kai kusan Naira 1,575. Tushen cinikin ya canja a kan layin, amma har yanzu gwamnati na sa ido a kai,” inji shi.
