Mu guji cin mutuncin Naira da raina alamomin ƙasa 

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ba da jimawa ba ne kafafen watsa labarai da zaurukan sada zumunta suka cika da labaran hukuncin da wata kotu a Kano ta yanke wa wasu fitattun ’yan jihar, shahararren mawaƙin Hausa, Hamisu Breaker, da fitaccen ɗan TikTok ɗin nan Al-Amin G-Fresh, sakamakon laifin mannin kuɗi a wajen biki, wanda hakan ya karya dokar da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya kafa a cikin shekarar 2024, wacce ta haramta amfani da mannin kuɗi a lokacin taro da bukukuwa. 

Idan ba a manta ba, harwayau a cikin shekarar da ta gabata wata Kotun Tarayya a Jihar Legas ta ɗaure wani shahararren mai fafutukar ’yancin canjin jinsin nan, kuma mai amfani da shafukan sada zumunta, wanda aka fi sani da Bobrisky, saboda laifin mannin kuɗi a wajen taron biki da wasu laifuka masu alaƙa da haka. Laifukan da ya amsa, kuma aka yanke masa hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari. 

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya haramta amfani da mannin kuɗi a hukumance, a matsayin wani ɓangare na matakan da bankin yake ɗauka don kare martabar kuɗin Naira da hana tauye darajarta. Wannan haramcin ya ƙara ƙarfi ne a cikin 2025 tare da fara aiwatar da hukunci ga masu karya dokar kamar yadda aka gani a shari’ar mawaƙi Hamisu Breaker da sauran su.

Tun a ranar 29 ga watan Agusta, 2025 Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta ƙasa (NOA) ta fara ƙaddamar da gangamin wayar da kan ‘yan Nijeriya kan martabar alamomin ƙasa. Wannan gangami an fitar da shi ne da nufin wayar da kai su gane kuskuren cin mutuncin alamomin ƙasa da rashin girmama su, na tsawon makonni biyu,. An gudanar da wannan gangami a dukkan jihohin ƙasar nan 36 har da Babban Birnin Tarayya Abuja, da kuma dukkan ƙananan hukumomi 774 na Nijeriya.

Gangamin ya mayar da hankali ne kan manyan fannoni guda biyar, ciki har da wayar da kai kan ƙimar alamomin ƙasa da kyawawan ɗabi’un ƙasa, wanda ya haɗa da ilimantar da mutane game da muhimmancin girmama tutar ƙasa, taken ƙasa, martaba kuɗin ƙasa, da sauran alamomin ƙasa a matsayin ginshiƙan haɗin kai da cigaban al’umma. 

Martaba kuɗin ƙasa, tutar ƙasa, da taken ƙasa, suna da matuƙar muhimmanci a kowacce ƙasa ta duniya. Duk wata ƙasa mai ’yanci tana da alamomin da suka bambanta ta da sauran ƙasashe, sannan hakki ne mai girma kowacce ƙasa ta girmama alamomin wata ƙasa. Doka ce  mai girma a ga wani mutum ɗan ƙasa ko baƙo yana aikata wani abu da za a iya danganta shi da rashin girmamawa ko cin mutuncin alamomin wata ƙasa. 

Akwai wata skekara da Nijeria da ƙasar Ghana suka buga wani wasan ƙwallon ƙafa wanda Allah Ya bai wa ’yan wasan Nijeriya nasara akan ƙasar Ghana, saboda jin daɗi da murna sai aka samu wasu matasa asalin ‘yan Nijeriya mazauna Ghana suka fita kan titi suna murna suna jan tutar Ghana a ƙasa suna ɗaga ta Nijeriya a sama, wannan abin da suka yi ya haifar da rikici sosai a unguwannin Zango na ƙasar, wanda har ya sa dangantaka ta fara tsami tsakanin ’yan Nijeriya da Ghana. Hakan kuma ya ƙara nuna mana muhimmancin da alamomin ƙasa ke da shi a idon al’ummar duniya. Don haka bai kamata mu a nan Nijeriya mu riƙa raina kima da darajar namu alamomin ba. 

ƙasa ita ce tushen rayuwa, kuma alamomin ƙasa na daga cikin manyan abubuwan da ke wakiltar ƙasa da haifar da haɗin kai, ƙaunar ƙasa, da ci gaban al’umma. A Nijeriya, ƙasarmu mai yalwar al’adu, harsuna da addinai daban-daban, akwai buƙatar a riƙa girmama duk wata alamar ƙasa domin tabbatar da zaman lafiya, haɓaka haɗin kai, da kuma ƙarfafa jin ƙaunar ƙasa a tsakanin ‘yan ƙasa. 

Harwayau, daga cikin alamomin da ake danganta su da kishin ƙasa ko cigabanta, sun haɗa da girmama tarihin ƙasa, ɗabi’un al’umma, da dokokinta, kamar yadda suke ƙunshe a cikin Kundin Tsarin Mulkin ƙasa. Kai, har ma da hoton shugaban ƙasa, lambobin ƙasa, da sauran alamu kamar ƙananan kayan tarihi da suka jima suna bayyana tarihi da al’adun ƙasa. Alamomin ƙasa suna taimakawa wajen angiza soyayya da ƙaunar ƙasa, da ƙara kwarjini da kimar al’ummar ƙasa a idanun sauran al’umma. A yayin da ’yan ƙasa suka rungumi wannan gangami, suka kuma girmama alamomin ƙasa, za a samu fahimtar juna da zaman lafiya a tsakanin su, da raguwar rikice-rikice da tashin hankali da ake fama da su a ƙasa, saboda duk wanda ya girmama ƙasarsa ba zai yi aiki da zai kawo cikas ga al’ummar ta ba.

Idan ’yan ƙasa suka riƙa kiyayewa da girmama alamomin ƙasa, hakan zai yi tasiri wajen haɓaka ɗabi’u masu kyau kamar ƙwarewa, mutunci, da amincewa a cikin ma’amaloli na yau da kullum. Sannan kuma idan har za mu riƙa girmama tutar ƙasarmu da rera taken ƙasa cikin shauƙi da nuna kishi a lokacin bukukuwa da tarukan al’umma, hakan zai ƙara ƙarfafa haɗin kai da haɗewar jama’a ba tare da la’akari da bambance-bambancen da muke da su ba.

Idan ’yan Nijeriya suka riƙa girmama alamomin ƙasa, hakan zai nuna wa sauran ƙasashe na duniya, cewa Nijeriya ƙasa ce mai mutunci da martaba. Wannan na taimakawa wajen gina suna mai kyau a idon duniya, kuma ya ba ƙasa damar samun haɗin kai da goyon baya wajen hulɗa da ƙasashen waje. Alamomin ƙasa suna da alaƙa da tarihi da al’adun mutanen ƙasa. Girmamawa da riƙewa da mutunci yana taimakawa wajen kiyaye tarihin ƙasa, kuma yana sa matasa su fahimci inda suka fito da kuma matsayin su a rayuwa. Wannan ne zai taimaka musu su zama masu kishin ƙasa da kuma kiyaye al’adunsu.

Lallai yana da muhimmanci ’yan Nijeriya mu haɗa kai da Hukumar NOA, domin tabbatar da ganin wannan gangami ya samu nasara da karɓuwa a ko’ina a faɗin ƙasar nan. Don ƙara kambama sunan ƙasarmu da kimarta, yadda duk inda aka ji taken Nijeriya, ko aka ga tutar ƙasarmu, za a jinjina mana. Kamar dai yadda muke gani a finafinan ƙasar Amurka, yadda suke martaba tutar ƙasar su da kare al’adunta da ƙudirorinta na tsare ’yancin ’yan ƙasa! 

Yana da muhimmanci a riƙa samar da shirye-shirye a makarantu da wuraren tarukan jama’a, domin koyar da matasa da al’umma muhimmancin girmama alamomin ƙasa. Wannan zai haifar da wayewar kai da kishin ƙasa wanda zai haifar da kyakkyawan tasiri a nan gaba.

Sannan, Gwamnati tare da sauran hukumomin masu ruwa da tsaki a wannan gangami su samar da tsauraran dokoki domin hana cin zarafin Naira, ko raina tutar ƙasa da taken ƙasa, da wulaƙanta sauran alamomin ƙasa. Dole a ɗauki matakai masu tsauri  na hukunta duk wanda ya tauye waɗannan alamu domin kiyaye mutuncin ƙasar nan, kamar yadda muke gani yana faruwa a ɓangaren fitattun mutane da jama’a ke yawan bibiyar al’amuransu a zaurukan sada zumunta. 

Kodayake, akwai zarge-zarge da ke nuna cewa ana zaɓar waɗanda ake hukuntawa ne don a zubar musu da mutunci, alhalin ana kawar da kai da abubuwan da masu kuɗi da manyan masu riƙe da muƙaman gwamnati ko iyalansu ke yi. Ya kamata doka ta shafi kowa, matuƙar ana so a samu nasarar samar da canjin kan da ake buƙata. 

Yana da muhimmanci a tabbatar da cewa alamomin ƙasa kamar tutar ƙasa da taken ƙasa suna tashi a manyan wuraren jama’a, kasuwanni, makarantu, da ofisoshi. A raba manya da ƙananan tutoci ga ɗalibai, ma’aikata, direbobi da sauran ’yan Nijeriya, don isar da wannan saƙo ga kowa da kowa. Sannan, kamar yadda muka ba da misali a baya game da yadda wasu ƙasashen irin Amurka suke yi ta cikin finafinan su, mu ma a nan Nijeriya, Hukumar Kula da Harkokin Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC) ta ƙarfafa gwiwar masu sana’ar shirya finafinai, don shigar da irin waɗannan manufofi na gwamnati a cikin labaransu. Haka ma mawaƙa, wasanni, da kafafen watsa labarai, ta cikin tallace-tallacen rediyo da talabijin, waɗanda ke nuna muhimmancin girmama alamomin ƙasa. Wannan zai taimaka wajen isar da saƙo mai kyau zuwa ga matasa da sauran al’umma a cikin harsuna daban-daban na ƙasa.

Girmama alamomin ƙasa ba wai ya tsaya ne kawai ga ɗaga tutar ƙasa ko rera taken ƙasa ba ne kawai, harwayau yana koyar da kishin ƙasa, kiyaye mutunci da tarihin ƙasa, tare kuma da ba da gudunmawa wajen gina Nijeriya mai ƙarfi da yaran mu na baya za, su yi alfahari da ita nan gaba.

By ukarofi