
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar Sojojin Nijeriya NA, ta fitar da saƙon ankarar da al’umma game da wani shafin ɗaukar aiki na bogi da aka buɗe da sunanta, cewa an fara ɗaukar ƙananan sojoji aiki a karo na 90.
Daraktan hulɗa da jama’a na ofishin ɗaukar aikinta, AU Hammanga ya ce shafin da ake yaɗawa na bogi ne domin a ruɗar da al’umma don haka ya yi kira ga jama’a da su yi watsi da shi.
Rundunar ta bayyana cewa za a samu sahihin shafin ɗaukar aiki ne daga kafafen labarai da ta amince da su, inda za a yaɗa wa al’umma da zarar an fara ɗaukar aiki a hukumance.
Kyaftin Hammanga ya ce, rundunar tana aiki tukuru wajen ganin an tabbatar da kiyaye gaskiya da adalci yayin ɗaukar aiki a harkokinta inda ta ankarar da jama’a su guji ƴan damfara.
Ya ƙara da cewa, za a iya ziyartar sahihin shafinta domin samun bayananai da suka shafe ta kai-tsaye.
