
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An garzaya da kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG, Luis Enrique zuwa asibiti bayan allon kafaɗarsa ta karye a wani mummunan hatsari da ya rutsa da shi.
PSG ta tabbatar da faruwar al’amarin a sanarwar da ta wallafa ta kafar X, inda ta ce ɗan Sifaniyar kocin mai shekaru 55 da ya jagoranci ƴan wasanta a lashe kofin Champions League, za a masa aiki bayan samun raunin a ranar Juma’a.
Tuni jami’an bada agaji gaggawa suka fara ba shi kulawa gabanin zuwa asibitin, inda za yi masa aikin gyaran karayar ƙashin kafaɗar nasa.
Ta kuma yi masa fatan samun waraka cikin lokaci gami da bada cikakken tallafi a gare shi.
Saidai ba a san ko mota ce ta buge shi ba a lokacin da ya ke tsaka da tuƙin kekensa kasancewar sa mai son tafiya a keke ko kuma faɗuwa ya yi da kansa.
A kakar wasan da ta gabata ne PSG ta lashe Kofin Zakarun Nahiyar Turai bayan doke Inter Milan da ci 5 da 0 a wasan ƙarshe.
