Gwamnatin Tarayya ta ƙara farashin gas na CNG daga N230 zuwa N380

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙara farashin sayar da iskar gas ta CNG daga N230 zuwa N380 akan ko wane mitar kubik (SCM).

A cewar Nairametrics, sabon farashin a Legas da Abuja ya fara aiki ne a ranar 1 ga Satumba, 2025, amma an riga an aiwatar da shi a wasu sassan ƙasar watanni biyu da suka gabata.

Kamfanoni masu zaman kansu da suka haɗa da NIPCO Gas da Mobil, sun daidaita farashin famfunan su daga N230 zuwa N380 akan kowace mitar kubik (SCM) a ranar Litinin 1 ga Satumba, 2025.

A wasu wuraren, farashin ya kai N500 a SCM saboda dalilai kamar nisa daga bututun mai, dogaro da rarrabawar manyan motoci, da kuma farashin mai.

Majiyoyin gwamnati sun tabbatar da faruwar lamarin, tare da lura da hakan wani ɓangare ne na ƙoƙarin daidaita farashin CNG a yankuna daban-daban.

“Daga ranar 1 ga Satumba, farashin CNG na kowane nau’in motocin fasinja zai kasance N380 kan kowane SCM a Abuja da Legas. A duk sauran wurare, an riga an sanya shi N380, watanni 2 baya,” inji majiyar.

Sai dai kuma, a gidan mai na NNPCL bai canja ba a N230 har zuwa ranar Talata, 2 ga Satumba, 2025.

Tafiyar CNG ta Nijeriya ta fara ne a shekarar 2023, bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi. Hauhawar farashin man fetur da dizal ne ya sa Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin Shugaban ƙasa na ‘Compressed Natural Gas Initiatiɓe’ (PCNGi) a matsayin madadin masu ababen hawa mai rahusa da tsafta.

A ƙarƙashin shirin, an bai wa direbobin ‘yan kasuwa canjin motoci kyauta a cibiyoyin da aka amince da su, yayin da jihohi irin su Legas, Ogun, Oyo, da Ribas suka ƙaddamar da motocin bas masu amfani da CNG da gidajen mai.

Ya zuwa tsakiyar shekarar 2025, fiye da tashoshi 65 sun fara aiki a cikin jihohi 21, tare da tallafin sama da dala miliyan 450 na zuba jari da horar da dubban masu fasaha.

A halin da ake ciki kuma, sabon farashin ya nuna cewa banbancin da ke tsakanin CNG da man fetur a yanzu ya kai kusan N300, inda ake sayar da man a tsakanin N855 zuwa N865 kowace lita a Legas, sai kuma kusan N890 zuwa N910 a Abuja.

Direbobin sun yi gargaɗin cewa hawan CNG na iya lalata fa’idar tsadar da yake da ita akan man fetur.

By ukarofi