Yadda ‘yan bindiga ke kare al’umma bayan an yi sulhu da su a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Bayan sulhu da aka cimma a ƙaramar hukumar Jibiya ta Jihar Katsina, ‘yan bindigar da ke addabar al’ummomin yankin yanzu sun koma kare su daga hare-haren ɓarayin daji dake riƙe da makamai.

Wani mazaunin ƙauyen Magama, Abubakar Mohammed, wanda ya bayyana hakan yayin wata hira da manema labarai ya nuna godiya bisa samun zaman lafiya da aka yi a yankin.

Yayin da yake bayani kan yadda zaman lafiya ya dawo, Mohammad ya tuna cewa kusan watanni shida da suka gabata aka cimma yarjejeniyar sulhu da ƴan bindigan.

Ya ce tun daga lokacin ba a sake samun wani hari daga ‘yan bindigan ba a ƙauyuka daban-daban na yankin.

Ya ce: “Yawancin waɗannan ’yan bindigan mun san su, muna zama a wannan yanki tare da wasu daga cikinsu, wasu ma abokan mu ne a da kafin su shiga wannan harkar.”

“Amma muna gode wa Allah da suka yanke shawarar rungumar zaman lafiya da kansu. Wasu daga cikinsu yanzu suna zuwa kasuwa, amma ba za ka taɓa ganin suna ɗauke da bindiga ba.”

“Idan ka shiga daji, za ka same su ɗauke da bindigoginsu suna kare mu daga hare-haren waje, musamman daga Zamfara ko wasu ƙananan hukumomin da har yanzu ba su rungumi tattaunawar sulhu ba.” In ji shi.

Mal. Mohammad ya bayyana halin yanzu a matsayin lokacin girbi mai albarka, domin da dama sun koma gonakinsu bayan sun daina zuwa tsawon lokaci saboda rashin tsaro.

By ukarofi