
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Amurka ta sanya ƙasashen Afirka 16 ciki har da Nijeriya a sahun waɗanda akwai barazanar shiga ga ƴaƴanta a watan nan na Satumba.
Ta ce, ta yi haka ne saboda ankarar da mutanenta da ke ƙasashen da masu niyyar tafiya sakamakon samun barazanar tsaro, rikicin siyasa da haɗarin kula da lafiyarsu a ƙasashen.
Ma’aikatar Harkokin cikin gida na Amurka ta bad gargaɗin ne a matakai huɗu da suka haɗa da kulawa yadda ya dace kafin yanke shawarar tafiya zuwa matakin ƙarshe da ya shawarci da kada a yi tafiyar saboda barazana ga rayuka.
Game da wannan rahoton, ƙasashen Afirka da gargaɗin ya fi tsanani akansu, ma’aikatar ta shawarce su da su yi amfani da mataki na uku wato ‘sake duba hukuncin yin tafiya’ da kuma na huɗu, wato ‘kada a yi tafiya’.
Musamman Amurka ta fitar da saƙon gargaɗin domin bai wa ƴaƴanta da ke ƙasashen waje kariya wajen ankarar da su tsaro, lafiya, da haɗarin siyasa da za su iya fuskanta a ƙasashen waje.
