Al’umma sun samu sa’ida bayan hauhawar farashi ya ragu da kaso 20 a Agusta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ana sa ran al’ummar Nijeriya su samu sauƙi a farashin kayayyaki yayin da ƙididdiga ta nuna matakin hauhawar farashi ya ragu da kaso 20 a watan Agusta a Nijeriya.

Wannan shi ne wata na biyar a jere da ake samun ragi a matakin hauhawar farashin a ƙasar.

A cewar, rahoton ofishin kula da sauyin farashi da cibiyar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta fitar a ranar Litinin, hauhawar farashi ya sauko da kaso 20.12 a watan Agusta, 2025 daga kaso 21.88 da aka samu a watan Yuli.

Hakan na nuna an samu saukar farashi da kaso 1.76 a wata ɗaya, wanda kuma ake cigaba da samu wata bayan wata tun daga hauhawarsa a watan Agustan 2024 inda ya kai matakin 32.15.

Farashin kayan abinci ya sauka zuwa mataki na 21.87 daga 37.52 a shekarar da ta gabata zuwa yanzu, kamar yadda rahoton ya bayyana.

Saidai duk da haka, NBS ta ƙalubalanci yadda har yanzu farashin kayayyaki musamman na abinci ba su sauko yadda ake tsammani ba musamman a yankunan jihohin Arewa da ke fama da matsalolin rashin tsaro da ƙarancin ababen more rayuwa.

By Babaji