Taron FAO: Ministan kasafi ya nemi ‘yan ɓasashen waje da su zuba jari a fannin noma

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Ministan Tsare-tsaren Kasafin Kuɗi da Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya yi kira da a zuba jari mai ɓarfi na ɓasa da ɓasa a fannin noma da bunɓasa ban-ruwa a Nijeriya, inda ya bayyana ɓasar a matsayin wuri mafi cancanta a duniya wajen saka hannun jari a harkar noma a wannan zamani.

Ya bayyana haka ne a wajen Bikin Buɗe FAO National & Sub-Regional Hand-in-Hand Inɓestment Forum to Enhance Agricultural Inɓestment in West Africa and the Sahel, inda Mataimakin Shugaban ɓasa, Maigirma Sanata Kashim Shettima, ya kasance baɓo na musamman na girmamawa.

Sanata Bagudu ya jaddada cewa lokacin da aka gudanar da taron ya yi daidai da umarnin Shugaban ɓasa Bola Ahmed Tinubu da kuma shirin Mataimakin Shugaban ɓasa na ɓara ɓarfin Nijeriya wajen karɓar manyan jarin ɓasa da ɓasa tare da jawo hankalin duniya kan irin saka hannun jari da ake buɓata a fannin noma da ban-ruwa.

Ministan ya bayyana cewa duk da cewa Nijeriya na da filayen noma masu faɗi da kuma yawan matasa, yawancin harkokin noma na dogaro da ruwan sama ne kawai, wanda hakan ke rage yawan amfanin gona. Ya ce idan aka kara faɗaɗa ban-ruwa, manoma za su iya yin amfanin gona sau biyu ko sau uku a shekara, wanda zai buɗe damar samun wadataccen abinci, samar da ayyukan yi da ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.

Ya ɓarada jaddada buɓatar gaggawar zamani wajen bunɓasa kiwon kifi, duba da yadda al’ummomin masunta ke dogaro da koguna da tabkuna masu iyaka wajen samun kamun kifi. Haka kuma ya bayyana ɓangaren kiwon dabbobi a matsayin fanni mai dumbin damar canza tattalin arzikin ɓasa wanda aka dade ana yin watsi da shi. Ya ce kafa Ma’aikatar Raya Kiwon Dabbobi kwanan nan wata manufa ce ta musamman domin mayar da ɓangaren kiwon dabbobi injin ci gaban tattalin arziki maimakon tushen rikici.

Yayin da yake duba waɗannan matsaloli a cikin muhallin yankin Sahel, Sanata Bagudu ya gargaɗi cewa babban ɓalubalen da yankin ke fuskanta shi ne ɓarancin saka hannun jari na tarihi da na zamani. Ya ce, saboda matsayinta na ɓasa mai yawan jama’a da filaye, Nijeriya ita ce mafi cancanta kuma mafi riba wajen zuba jari a harkar noma da ban-ruwa a yankin Sahel da Afirka ta Yamma.

Ministan ya yaba wa Hukumar Abinci da Noma ta Duniya (FAO) bisa shirya wannan taro tare da bayyana jajircewar gwamnatin Nijeriya wajen jan hankalin al’umma da samar da kudaden saka hannun jari na duniya domin tabbatar da wadataccen abinci, samar da ayyukan yi da tabbatar da zaman lafiya a yankin ɓarɓashin jagorancin Shugaba Tinubu da Mataimakin Shugaban ɓasa Shettima.

By ukarofi