Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Uwargidan gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta tallafawa iyalan da suka haifi ‘ya’ya uku da aka haifa kwanan nan a garin Mada da ke ƙaramar hukumar Gusau.
A cewar sanarwar da sakatariyar yaɗa labaran uwargidan gwamnan, Rabi Yusuf ta fitar, ta ce an tallafawa iyayen da tallafin magunguna, kayan abinci, diapers, tallafin kuɗi da sauran muhimman abubuwa domin sauƙaƙa nauyin kula da jariran.
Suma a nasu ɓangaren, Iyayen ‘yan ukun Iliyasu Nuhu Mada da Aina’u Musa sun yabawa uwargidan gwamnan bisa kulawa dasu, inda suka bayyana hakan a matsayin wani babban ƙwarin gwiwa ga ɗaukacin iyalan su.
Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta jaddada ƙudirinta na ci gaban mata da ƙananan yara a faɗin Jihar Zamfara, inda ta bada tabbacin cewa ofishinta zai ci gaba da tallafawa marasa galihu da kuma inganta lafiyar mata da ƙananan yara.
