
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Al’amarin tsaro a Jihar Benuwai ya ɗauki wani salo yayin da a yau Litinin hukumomi suka gano gawarwakin ƴan sanda guda takwas da suka ɓata bayan halaka su a daren Juma’a wayewar Asabar.
‘Yan sandan sun rasa rayukansu ne yayin da ƴan bindiga suka farmake su a yankin Agu Centre da ke iyakar tsakanin ƙananan hukumomin Katsina-Ala da Ukum.
Rahotanni sun bayyana cewa harin shi ne mafi muni a ƴan watannin nan da aka yi wa jami’an tsaro wanda da fari ƴan sanda uku ne suka rasu kana daga bisani aka gano gawarwakin takwas.
A lokacin da al’amarin ya faru, jami’an haɗaka da suka haɗa da na ‘Operation Zenda’ da ‘Benue State Civil Protection Guard’ da kuma ‘Special Intervention Squad’ ne suke bakin aiki.
Da yake zantawa da manema labarai ta wayar hannu, Shugaban Ƙaramar Hukumar Katsina-Ala, Dakta Justine Shaku ya tabbatar da cewa an gano gawawwakin ne yayin da ake gudanar da wani atisayen nemo jami’an bayan ɓatan da suka yi.
Haka ma Kakakin ƴan sandan jihar, Udeme Edet shi ma a wata sanarwa ya jaddada haka, inda kuma ya tabbatar wa al’umma cewa jami’an tsaro suna aiki tuƙuru wajen ganin an samu zaman lafiya a yankin, wanda ke fama da matsalolin taɓarɓarewar tsaro.
