
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da yi wa wasu jami’an gwamnatinsa garambawul.
A wata sanarwa da Kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar, matakin na ɗaya daga cikin ƙoƙarin da ake yi na inganta harkokin mulki a jihar.
A umarnin da Gwamna ya bayar Antoni-Janar kuma kwamishinan shari’a, Barista Haruna Isa Dederi an mayar da shi Ma’aikatar Sufuri yayin da Babban Lauya kuma Babban Sakataren Ma’aikatar Barista Mustapha Nuruddeen Muhammad ya koma Ma’aikatar muhalli a matsayin babban sakatare.
Shi kuwa Kwamishinan Harkokin Jinƙai, wanda ya riƙe muƙamin mai riko Ma’aikatar Sufuri, zai koma na dindindin a ma’aikatar.
Gwamnan ya kuma umurci dukkan jami’an da sauyin ya shafa da su miƙa lamuran ofisoshinsu ga babba jami’i na ma’aikatar za su bari zuwa yau Talata.
