
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya nesanta kansa daga kalaman da aka jingina masa na soki burutsu da wani mai suna Kola Johnson da ya yi bayan ikirarin shi mai taimaka masa ne akan harkokin yaɗa labarai.
A cikin saƙon, wanda aka baza wa duniya a ranar Laraba, an ce wai Atiku ya yi alƙawarin fifita buƙatun Yarabawa idan aka zaɓe shi a matsayin Shugaban Ƙasa a zaɓen 2027.
Haka kuma, saƙon ya ƙunshi cewa gwamnatin Atiku za ta fifita wata ƙabila ɗaya cikin ƙabilun Nijeriya, yana mai ba misali da auratayya da ke tsakanin tsohon shugaban ƙasar da yankin Kudu maso Yamma.
Saidai, a yayin martani game da zantukan a yau Alhamis, sahihin mai taimaka wa Atikun akan harkar yaɗa labarai, Paul Ibe a wata takarda, ya ce mai gidansa ya bayyana kalaman Johnson a matsayin abinda aka ƙirƙira da ba shi da asali ko makama domin a ruɗar da al’umma.
Ya ce, bai taɓa alaƙa da Johnson ba ta fuskar mataimaki, mai bada shawara ko kusanci akan wani abu, don haka dukkan wani saƙo daga gare shi akan Atiku, ba gaskiya ba ne.
Jigon Jam’iyyar na PDP ya kuma zargi Fadar Shugaban Ƙasa da ɗaukar nauyin wasu ƴan baranda da nufin ɓata wa ɓangaren adawa siyasarsu.
Kazalika, ya yi kira ga ɗaukacin ƴan jarida da al’ummar ƙasa da su kawar da kai tare da tabbatar da rahoto gabanin amincewa ko yaɗa shi.
