Gina ɗakin karatu: ’Yan Nijeriya sun tara wa Remi Tinubu biliyan N20

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

’Yan Nijeriya, masu kuɗinsu da talakawa masu kishin ƙasa, sun tara wa uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu Naira Biliyan 20.

Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ce ta ke karɓa tare da tattara kuɗin da ake turawa a ƙarƙashin ‘gidauniyar ilimi ta Oluremi a 65.’

An ruwaito cewa, uwargidan shugaban ƙasar ce da kanta ta nemi ‘yan Nijeriya, masu kishin ƙasa, su tara mata wannan kuɗi.

A lokacin da take shirye-shiryen bikin cika shekaru 65 da haihuwa, Oluremi Tinubu, ta yanke shawarar cewa ba za ta yi bishasha ba.

Maimakon ‘yan Nijeriya, masu kuɗinsu da talakawa masu kishin ƙasa su riƙa tura mata kyaututtuka na murnar haihuwa, ta ga dacewar su yi mata karo-karon kuɗi.

Uwargidan Shugaba Bola Tinubu ta ce, za ta yi amfani da dukkanin kuɗin da aka tara wajen kammala gina babban ɗakin karatu na ƙasa a Abuja.

A cikin sakon bidiyo da ta fiyar, tsohuwar sanatar ta ce za ta sadaukar da ranar da aka haife ta, 21 ga Satumba, da abin da za ta tara, wajen gina ɗakin karatu don bunkasa ilimin ‘yan ƙasa, maimakon yin bushasha.

A cewar uwargidan shugaban ƙasar, kammala gina ɗakin karatu na kasa zai zama babbar kyautar ƙarin shekara a gare ta.

Yayin da take jawabi ga manema labarai a fadar shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu ta ce ta taɓa zama mambar kwamitin ilimi na majalisar dattawa, kuma ma’aikatar ilimi ba ta iya gina ɗakin karatun ba.

Ta ce, ga yara manyan gobe da ke tasowa, ɗakin karatun zai taka muhimmiyar rawa wajen saita tunaninsu, kuma ba ta ji daɗin yadda aka gaza gina ɗakin ba duk da an ƙaddamar da ginin a lokacin Shehu Shagari.

Oluremi Tinubu ta ce, za ta yi amfani da dukkanin kuɗin da ta samu don ƙarasa gina ɗakin karatu na ƙasa.

Uwargidan shugaban ƙasar, ta kuma yi martani ga waɗanda suka fito suna sukar shirinta na haɗa kuɗi don gina ɗakin karatu na ƙasa.

Daga cikin masu sukar, akwai Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, wanda ya wallafa a shafinsa na ɗ cewa:

“Na kaɗu matuka da na ga ta gabatar da buƙata cewa: maimakon a wallafa saƙonni taya ta murna, masoya su haɗa mata kuɗi don ta kammala gina ɗakin karatu na ƙasa a Abuja.

“Yayin da wannan buƙatar take ɗauke da tata muhimmancin, a hannu ɗaya kuma, wannan cin fuska ne ga kasar mu.

“Abin kaɗuwar shi ne, yadda a ƙasarmu, ake ɓatar da biliyoyin kuɗi wajen sayen jiragen ruwa na alfarma, gidaje da tafiye-tafiye waje, da dai sauran alatu na rayuwa, abin takaici ne ace wai da kuɗin taya murnar haihuwa ne za a kammala gina ɗakin karatu na ƙasa.”

Peter Obi ya sake jaddada mamakinsa na yadda ƙasa kamar Nijeriya ke bugewa a ‘maular’ kuɗin da za a gina ɗakin karatu, alhalin shugabanni na kashe tiriliyoyin kuɗi a samawa kansu rayuwar alfarma.

Da take martani, uwargidan shugaban ƙasa ta ce ya kamata ‘yan Nijeriya su yi koyi da kalaman tsohon shugaban Amurka, wanda ya ce ‘yan ƙasa su daina tunanin abin da ƙasarsu za ta yi masu, su dawo tunanin mai za su yi wa ƙasarsu.

By ukarofi