Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Dr. Bashir Usman Ruwan Godiya ya bayyana cewa aikin jarida shi ne ginshiƙin da ke hura rai ga dimokuraɗiyya tare da bunƙasa al’umma, inda ya kwatanta jarida da gada tsakanin shugabanni da talakawa.
Ya bayyana haka ne a yayin wata lacca a Katsina, a cigaba da bikin zagayowar shekaru 38 da ƙirƙirar Jihar Katsina da Ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa (NUJ), reshen Katsina ta shirya.
Dr. Ruwan Godiya ya ce ba za a iya cimma nasara ba, ba tare da jarida ba, kasancewar jarida ita ce ake kira “ɓangare na huɗu na gwamnati” tare da majalisar zartarwa, da kuma ɓangaren shari’a.
Ba tare da jarida ba, dimokuraɗiyya ba za ta yi aiki ba. Shugabanni ba za su iya bauta wa al’umma ba, haka kuma jama’a ba za su iya fahimtar shugabanninsu ba sai da jarida,” in ji shi.
Ruwan Godiya wanda tsohon mai ba gwamna shawara kan manyan makarantu a jihar,ya yi suka kan tsohon tsarin bayar da rahoton jarida da ke fifita manyan ’yan siyasa da shugabanni, tare da watsi da batutuwan al’umma a ƙasa. A cewarsa, hakan na raunana dimokuraɗiyya tare da hana talakawa damar yin magana.
Harwala yau Ruwan Godiya malamin aikin jarida,ya yi kira da a sauya salo zuwa “Jaridar Ci gaba” wato nau’in bayar da rahoto da ke ƙarfafa gaskiya, riƙon amana, tattaunawa, da kuma samar da ci gaban jama’a a fannoni daban-daban.
“Ƴan jarida dole su tabbatar da cewa muryar talakawa ma na tasiri ba kawai ta shugabanni ba kuma a yi amfani da jarida wajen sauya al’umma, a bunƙasa ta a dukkan fannoni zamantakewa, tattalin arziƙi, addini da siyasa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa dole ’yan jarida su kasance masu dabarun tsari a aikinsu, kamar yadda rundunar soji ke tsara dabarun yaƙi. Ya ce hakan kaɗai ne zai tabbatar da cewa aikin jarida zai ciyar da al’umma gaba tare da haɗa shugabanni da jama’a.
Tunda farko sai da shugaban ƴan jarida reshen Jihar Katsina Hassan Tukur Dan Ali ya jinjina ga gwamnan Katsina bisa goyon baya da taimako da ya ke bai wa ƙungiyar a duk lokacin da suka je masa.
Haka kuma ya yaba da kyakkyawar dangantaka da ke tsakanin gwamnatin jihar Katsina da Yan jarida a jihar.
Shima shugaban yan jarida na ƙasa ya yi Dr Al Hassaan Yahya Abdullahi ya faɗi ƙoƙarin da ƙungiyar ke yi wajen inganta rayuwar ya’yan ƙungiyar.
Ya bayyana cewa yanzu haka ƙungiyar ƴan jarida na kasa na shirin farfaɗo da inshorar lafiya da sabon tsarin albashi ga ƴan jarida a faɗin ƙasar.
Shugaban taron kuma Uban ƙungiyar a Jihar Katsina wazirin ilimin ƙasar Hausa Farfesa Sani Lugga ya buƙaci gwamnatin jihar da ta sake duba yadda ake gudanar da ƙananan hukumomi ke gudanar da zaman sulhu da ƴan bindiga.
Ya bayyana cewa yan sulhu da ƴan bindiga ba tare da sun ajiye makami ba,ya nuna cewa alumma su suka bada kai bori ya hau.
Wakilan gwamna a wajan taron kuma kwamishinan yaɗa labarai, Dr Salisu Bala Zango ya faɗi wasu cigaba da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta samu a fannoni da dama.
Ya yaba da kyakkyawar dangantaka da ke tsakanin gwamnatin Katsina da yan jaridu a jihar.
Kwamishinan ya tabbatar wa ƙungiyar da NUJ a jihar cewa Gwamnatin Dikko Raɗɗa za ta cigaba da aiki kafaɗa kafaɗa da ƙungiyar don kowa cigaba a jihar.
