Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mai ba gwamna shawara kan harkokin jam’iyyun siyasa a Katsina Malam Shafi’u Ruwan ya ce ‘yan bindiga ne suka nemi sulhu da al’ummomin yankunan da ke fama da rashin tsaro,saɓanin lokacin gwamnatin baya da Mustapha Inuwa ya riƙe muƙamin sakataren gwamnati.
Duwan na mai da martani ne kan maganar da madugun jam’iyar ADC a Katsina Mustapha Inuwa wanda ya soki yadda ake gudanar da sulhu da ‘yan bindiga ba tare da sun ajiye makami ba.
Ya ce ƙananan hukumomi 8 da suka rungumi sulhu da yan bindigan,”Su yan bindigan suka buƙaci haka, sabanin gwamnatin su da suka shiga daji suka kwaso yan bindigan zuwa gidan gwamnati da sunan sulhu aka biya su daga baya aka mayar da su daji.
“Haka aka maida su daji basu ajiye makamai ba kuma basu bar ta’addanci ba,”inji Shafi’u Duwan.
Ya tunatar da Mustapha Inuwa cewa lokacin da ya riƙe muƙamin shugabancin kwamitin tsaron a jihar kowa yasan rawar da ta taka.
Duwan ya bayyana cewa a duk jihohin da ke fama da ƙalubale na tsaro babu jihar da ta ɗauki matakai na kawo ƙarshen matsalar tsaro irin Jihar Katsina ƙarƙashin mulkin Dikko Raɗɗa.
“Gwamna Dikko Raɗɗa ya ɗauki dubban matasa aikin samar da tsaro na CWC da suka fito a ƙananan hukumomin da ke fama da ta’addanci wanda yana ɗaya da abin da yasa ‘yan bindiga suka fara neman sulhu,”inji shi.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Dikko Raɗɗa ta sayi motocin yaƙi da baburan hawa tare da sauran kayan yaƙi da aka rabawa jami’an tsaron CWC da sauran jami’an tsaro domin yaƙi da ta’addanci a ƙananan hukumomin da ke fama da hare haren ‘yan bindiga a jihar.
“Limaman Juma’a, Ladanai da masu unguwanni gwamnatin Dikko Raɗɗa tuni ta fara biyan su alawus a duk wata,suma hakimai, gwamnati ta mai da su matakan albashi na 16(Grade level 16) duk wannan mataki ne na kawo zaman lafiya a jihar.
Sai Duwan ya ƙalubalanci Mustapha Inuwa da ya fito ya faɗi abinda su kayi na ɗakile hare haren ta’addanci duk da biliyoyin Naira da suka kashe.
Ya ce mutane su sani babu ruwan gwamnatin Katsina da shiga cikin zaman sasancin da ke wakana a ƙananan hukumomin, sai gwamna Dikko Raɗɗa ya sha nanatawa idan yan bindiga ne suka ne mu sasancin to gwamnati a shirye ta ke ta shiga cikin lamarin.
Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su ba gwamnatin Dikko Raɗɗa goyon baya a ƙoƙarin da take wajen kawo ƙarshen ta’addanci a jihar.
A kwanakin baya ne Mustapha Inuwa ya soki yadda ake gudanar da sulhu da ƴan bindiga ba tare da sun ajiye makamai ba.
