Fashi: Yadda ’yar jarida ta rasa ranta sakamakon tsirgowa daga bene hawa uku a Abuja

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kwamishinan ‘yan sanda na Babban Birnin Tarayya Abuja, CP Ajao Adewale, ya tabbatar da cewa Somtochukwu Maduagwu, ’yar jaridar gidan talbijin na Arise News ta rasa ranta ne bayan ta faɗo daga hawa na uku na gidanta a wani hari da wasu ‘yan fashi da makami suka kai a Katampe, Abuja.

An bayar da rahoton cewa, lamarin mai ratsa zuciya ya afku ne da sanyin safiyar ranar Litinin a Unique Apartments, wani tagwayen bene mai hawa uku mai ɗauke da gidaje 18 da ke yankin Katampe a ƙarƙashin yankin Mabushi.

Yayin da ya ke magana a ranar Laraba yayin da ya bayyana a gidan talabijin na Arise TV, CP Adewale ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun isa wurin inda suka tarar da Maduagwu a sume a ƙasa.

“’Yan sanda sun je wurin da lamarin ya faru, suka same ta a kwance a sume, nan take aka kai ta babban asibitin Maitama, inda likitoci suka yi ƙoƙarin farfaɗo da ita ta hanyar amfani da CPR, abin baƙin ciki sai rai ya yi halin sa,” inji shi.

Kwamishiniyan ya tabbatar da cewa ‘yar jaridar ‘yar shekaru 29 ta yi tsalle daga gidanta mai hawa uku a ƙoƙarinta na tserewa bayan da wasu ‘yan fashi da makami suka mamaye harabar gidan.

A cewar rahoton ‘yan sandan, maharan sun samu shiga cikin ginin duk da kasancewar jami’an tsaro guda biyu. ɗaya daga cikin masu gadin ya yi yunƙurin tinkarar maharan amma an harbe shi ya kuma raunata a yayin aikin.

“A cikin firgicin da ya biyo baya, Maduagwu, wadda ke zaune a saman bene, ta yi tsalle daga hawa na uku,” inji Adewale.

Mazauna yankin sun ce ’yan banga da makwabta da farko sun gano ta a sume kafin ‘yan sanda da jami’an lafiya su iso.

CP Adewale ya bayyana cewa an kafa wata tawagar bincike ƙarƙashin jagorancin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda (bincike) don bin diddigin masu laifin.

“Mun kafa wata tawaga ta musamman mai bincike ƙarƙashin jagorancin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, bincike, tare da duk wani ɓangare na dabara domin gano masu laifin.

Somtochukwu Maduagwu, wadda abokan aikinta ke kiranta da Sommie, an bayyana ta a matsayin tauraruwa mai tasowa a aikin jarida a Nijeriya. Mutuwarta ta jefa ma’aikatan jaridar Arise News da sauran kafafen yaɗa labarai cikin alhini.

Kwamishinan ‘yan sandan ya jajanta wa ‘yan uwanta, yana mai cewa: “Rundunar ‘yan sandan Abuja ta sake jajanta wa iyalan Sommie, da abokan aikinta na Arise, da ‘yan Nijeriya da suka raɗaɗi.”

Lamarin dai ya ƙara dagula al’amuran da suka shafi munanan laifuka da rashin tsaro a Abuja, musamman ma a gidajen zama da a da ake ganin babu wata matsala.

Yayin da ake ci gaba da bincike, ‘yan Nijeriya na neman a gaggauta neman wa Somtochukwu adalici tare da ɗaukar tsauraran matakai na tabbatar da tsaron lafiyar ‘yan ƙasar a babban birnin ƙasar.

By ukarofi