
Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana Boko Haram a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen tsaro mafi rikitarwa da Nijeriya ta taɓa fuskanta. Ya ce, a wasu lokutan ma ‘yan ta’addan su kan fi sojojin ƙasar makamai.
Jonathan ya bayyana haka ne a Abuja yayin ƙaddamar da littafin ‘Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum’ na tsohon Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Lucky Irabor (mai ritaya).
Sabanin rikicin Neja-Delta da sauran tarzoma, Jonathan ya ce matsalar Boko Haram ta bar mummunan tabo saboda tsaurin akidunsu, tallafin ƙasashen waje da kuma kayan yaƙin zamani da suke da shi.
Ya kuma tuna cewa sace ɗalibai mata na Chibok a 2014 ya kasance ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi ba shi raɗaɗi a mulkinsa, abin da ya ce ba zai taɓa gogewa daga tarihin ƙasar ba.
Ya jaddada cewa ba za a iya ɗaukar Boko Haram a matsayin ƙaramin matsalar tsaro kawai ba, dole ne a bi ta da dabarar haɗin gwiwa wacce ta haɗa tsaro da ingantaccen mulki, rage talauci da kuma ƙarfafa matasa.
Taron ya samu halartar manyan baki ciki har da tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, tsohon mai ba da shawara kan harkokin tsaro Janar Babagana Monguno (rtd.), ministoci, jakadu da kuma sarakunan gargajiya
