Gwamna Raɗɗa ya kai ziyarar ba-zata wata makarantar sakandare a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar katsina Dikko Umaru Raɗɗa ya kai ziyarar ba-zata zuwa makarantar kwana ta maza da ke garin Ɓatagarawa don ganin yanayin makarantar da kuma ɗaliban.

Gwamna ya kuma zagaya cikin makarantar domin ganin halin da ɓangarorinsa yake ciki har da madafar abinci.

Da ya ke jawabi ga ɗaliban makarantar gwamnan ya hore su da su zama mas ladabi da biyayya da kuma bin dokokin makaranta.

Wannan ziyara ta bazata ita ce ta farko da gwamnan Raɗɗa ya fara kaiwa domin gane ma idanunsa halin da ɗalibai ke ciki.

Ya kuma kira garesu da su himmatu wajan karatu domin zama shugabannin gode.

Malam Dikko Raɗɗa ya duba ɗakin dafa abinci inda ya yaba da inganci da kuma tsabta na abincin da ake dafawa ɗaliban bayan ya ɗanɗana.

Ya yi wa ɗaliban albishirin cewa gwamnatinsa za ta ƙara yawan kayan abincin da ake basu.

By Babaji