
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mai Shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya yi watsi da ƙara akan Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da ke ƙalubalantar halascin dakatarwar wata shida da aka yi wa sanatar da ke wakiltar Jihar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan a majalisar kan rashin biyayya ga dokoki.
Alƙalin ya yanke hukuncin ƙarar ne, wadda Ovavu Illiyasu da wasu tara suka shigar sakamakon masu ƙarar ba su da hurumin kawo ƙarar a gaban kotu, don haka bai samu tushe ba a shari’a.
Channels TV ta ruwaito cewa masu ƙarar sun nemi kotu ta haramta dakatarwar da Majalisar Dattawa ta yi wa Sanatar, inda ake zargin ta da take wasu ƙa’idoji da rashin bin doka.
Saidai a gaban kotu an bayyana cewa babu wanda daga cikin masu ƙarar ya nuna cewa shi wakili ne na majalisar ko wani hukuma da ke da ikon ƙalubalantar irin wannan mataki.
Kotun ta jaddada cewa irin waɗannan ƙarar da suka shafi matakan majalisa suna buƙatar shigarwa ne a Kotun Ƙoli ko kuma ta hannun wadanda suka samu izinin doka, don haka ta kori ƙarar har sai an bi hanyoyin da doka ta tanada.
Haka kuma za a cigaba da sauraron duk wasu matakai na gaba idan masu ƙarar sun bi hanyar da doka ta amince da ita.
