Laifin talaka ne ko na shugabanni?

Spread the love

Duk wahalar da talakawa ke sha a Nigeriya ba damuwar akasarin shugabanni bane tunda har yau cewa su ke yi za su tallafa da kuɗi da abinci na wucin gadi. Sauran lokacin kuma ba a san wa zai taimaka ba. Duk da haka maganar talaka da malamai laifin mu ne mu gyara halayen mu, sun manta sace dukiyar talaka da rufe kan iyakokin ƙasa sun hana ayyukan yi da shigo da kayan buƙata da karya darajar naira da cire tallafin mai su kaɗai suka rikita Nigeriya ko talaka na da hannu a kan su.

Musamman ‘yan arewa mu faɗawa juna gaskiya mutanen mu suka assasa komai ana ganin su waliyi ne idan an ce su gyara talaka shi zai fara zagin ka, shi ya sa TUC da NLC suke ko oho da komai, ta yaya kasa za ta gyaru.

Ko talaka zai kwana cikin masallaci da coci don tsoron Allah idan shugaba zai ɗauki albashin milyoyi a wata wani kuma ya sace milyoyi, ɗan majalisar da ka zaba ya gudu baka sake ganin sa ba kuma bai damu da cewar a sassauta manufofin tattalin arziki ga talakawa ba ta yaya talaka zai samu sauƙi.

Duk masifar da ake ciki janye tallafin Mai ya jawota to ina dalilin da ba za a maida tallafin ba kowa ya huta tunda sun kasa faɗan mutum daya mai cin tallafin man bayan talaka.

Shugabanni su sani adduar wanda aka zalunta bata faɗuwa a banza komai daɗewa idan Allah ya waiwaice su tallafin Allah zai iske talaka ta inda ba sa zato kuma In Sha Allah za su zamo kamar a yi ruwa a ɗauke sai tarihi su da masu kare su ko tallafa musu zalunci baya tabbata.

Talakawa aci gaba da addu’ah wanda suka assasa wahala da wanda suka aiwatar da masu amfana da masu Jin daɗi da masu ganin ba komai bane babu abin da zai faru ya Allah ka karya su ka mana maganin su a ruwan sanyi Allah ka bamu mafita.

Daga Muazu Hardawa, Unguwar Fadamar Mada, Bauchi. 08062333065.

By ukarofi