Gwamnatin Tinubu na dukan ‘yan Nijeriya da ɗanyen kara – Mustapha Tinubu 

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An bayyana Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da cewa mutum ne mai son cigaban al’umma  amma sai dai ba shi da mashawarta a gwamnatinsa masu kishi, da a ce akwai irinsu Dakta Rabiu Musa Kwankwaso jagoran Kwankwasiyya a kusa da shi da talaka ya yi sambarka saboda zai kawo gyara.

Hon. Mustapha Muhammad Tinubu (Chiranchi) jigo a tafiyar Kwankwasiyya a jihar Kano ne ya bayyana hakan da yake zantawa da manema labarai bayan ɗaurin aure da aka yi na ‘ya’yansa.

Mustapha Tinubu wanda ya bayyana cewa sunansa da ake laƙanawa da Tinubu a ciki ya samo asali ne saboda zama da suka yi da shugaban ƙasa na yanzu Bola Ahmad Tunibu a shekarar 1999 a Agege a jihar Legas yana ɗaya daga cikin yaransa, wannan shine abinda ya kawo ake kiransa da sunan sai kuma ya yi tasiri.

Sai dai Hon. Mustapha Muhammad Tinubu ya ce sai dai ga shi ƙarƙashin gwamnatin Ahmad Bola Tinubu na tarayyar ƙasar nan ana ta  tafkar yan Nijeriya da ɗanyen kara, wannan abin kaico ne sai dai  suna fata Allah ya saisaita shi ya shigo da irinsu  jagoransu injiniya  Dakta Rabiu Musa Kwankwaso su saita ƙwaƙwalensa su saita tafiyar sa a kori waɗanda suke kyamar   cigaban talaka.

Da yake magana akan masu cewa yana hidima ga tsarin Kwankwasiyya  tun a baya  har yanzu da suke  da Gwamnati amma ba wani abu na muƙami da aka bashi, ya ce komai da aka gani yin Allah ne kuma Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf yana sane dasu, komai lokaci ne ,duk abinda kaga ya zo maka  daga Allah ne lokacin da ne ya zo, ba makawa sai an yi shi,suna godiya ga Jagoran Kwankwasiyya da Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa irin kulawa da ake basu.

Alhaji Mustapha Muhammad Tinubu ya  kuma  musanta cewa akwai yan adawa da suke zabarinsa ya koma cikinsu, yace  duk wanda ya ce ma zai zabarin sa zai wahaltar da kansa ne, sai dai idan  ma ta kama ma jagoransu na  Kwankwasiyya ya shiga APC ɗin, za su bishi saboda zai gyara mata yanayi ne ,ta zama mai tsafta da talakawa za su amfane ta, don haka shi  babu ma wani mutum da zai dubi   idon ma da zai ce zai  zabareshi a matsayinsa na ɗan Kwankwasiyya.

Alhaji Mustapha Muhammad Tinubu ya yi godiya ga Allah da gwamnan jihar Kano bisa turo wakilai da ya yi zuwa ɗaurin auren da aka yi kuma ba abinda zai ce al’umma  sun amsa kira Allah ya saka da alkhairi.

Mustapha Muhammad Tinubu ya ce kullum suna zaune da jama’a lafiya kuma suna godiya ga Allah da ya haɗa kansu a tsarin tafiyar Kwankwasiyya suna tare tsintsiya maɗaurinsu daya ƙarƙashin jagora Dakta Rabiu Musa Kwankwaso.

Alhaji Mustapha Muhammad Tinubu ya godewa hadiman Gwamna irin kwamishinoni da  masu baiwa Gwamna shawara da shugabannin ƙananan hukumomi waɗanda suka sami  zuwa  ta ya shi murna da waɗanda suka yiwo aike Allah ya saka musu da alheri.

By ukarofi