Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
A ci gaba da kai ziyarar girmamawa da nufin tattaro shawarwari da za su haɓaka kasuwanci a Karamar Hukumar Bichi, ƙungiyar ‘Yan Kasuwa ta Bichi Traders Multi-Purpose Cooperatiɓe Society Limited ta samu ganawa da Shugaban sashen Ilimi na Cibiyar Al-furƙan Foundation Kano, kuma na’ibin limamin Masallacin Juma’a na FCE (T) Bichi, Malam Ashiru Abdulkadir Yakasai.
Malam Ashiru Yakasai, ya yi musu fatan alheri da jan hankali, akan su kasance masu haƙuri da tsoron Allah a cikin kasuwancinsu kuma su guji shirya abinda zai gurbata tunanin matasa da sauran al’umma, kamar yadda Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta ƙaramar Hukumar Bichi, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta bayyana a wata takarda.
A wani ɓangare, ƙungiyar ta kai ziyarar ga babban malami kuma uba, wato Sheikh Ishaƙ Bichi, wanda ya yi musu addu’a bisa canjin gurin kasuwanci da suka samu da fatan Allah ya sa hakan ya zama alheri a gare su.
Haka kuma, tawagar ta kai ziyarar ta’aziya bisa rashin mahaifiya ga Hon. Khalifa Ahmad MD na Hukumar Kula da ƙananan ‘yan kasuwa, wato Hajiya Aisha, inda suka yi addua da roƙon gafarar Allah a gare ta gami da fatan Allah ya albarkaci abinda ta bari ya kuma bada haƙurin rashinta.
A wani ɓangare na labarin, ƙungiyar ta yaba wa shugaban ‘yan sanda a babban ofishin rundunar na Bichi (DPO), SP Murtala Muhammad Fagam, tare da dukkan jami’an tsaro na Bichi.
A yayin kai masa ziyara a ofishinsa da ke ƙaramar hukumar, bisa kyakkyawar karbar da ya yi musu tare da yi musu alƙawarin gudanar da aiki kafaɗa da kafaɗa da ƙungiyar tare da isar da bukatunsu ga mahunkata, domin tabbatar da ci gaban kasuwar da garin Bichi baki ɗaya, ya kuma nemi izinin bude ofishin ‘yan sanda a cikin kasuwar bisa sahalewar Kwamishina ‘Yan Sanda na Jiha.
Sauran waɗanda ta kai wa ziyara sun haɗa da; mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda Mai Kula da Shiyyar Bichi, ACP Yusuf Dahiru Alkali, wanda ya zame musu uba sakamakon magance matsalolinsu da yake ƙoƙarin yi, sai ofishin Jami’an Tsaro na Farin Kaya DSS da ɓigilante Group Bichi Zone da malamai na addini; Malam Lawan Mai Nasara, shugaban Majalisar Malamai na JIBWIS da Malam Muhammad Ahmad limamin masallacin juma’a na titin Gwarzo.
ƙungiyar ta bayyana wadannan mutane a matsayin ‘yan kishin kasa, jajirtattu masu kishin al’umarsu da jama’ar Bichi baki ɗaya, inda ta sake ƙudirar aniyar kai irin wannan ziyarar ga malamai da iyayan kasa da jami’an tsaro da shuwagabanni da jagorori na Bichi baki ɗaya.
