Ya kamata a ba ƙabilar Ibo damar shugabantar ƙasar nan – Alhaji Aminu Abdullahi

Spread the love

Daga HABU ƊAN SARKI a Jos

Wani jigo a Jam’iyyar PDP ta Jihar Filato, kuma tsohon shugaban jam’iyyar a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, Alhaji Aminu Abdullahi ya bayyana buƙatar ýan Nijeriya su bai wa duk wani jajirtaccen ɗan takara daga ƙabilar Ibo damar zama shugaban ƙasa na gaba, bayan kammala wa’adin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Alhaji Aminu wanda yake ɗaya daga cikin shugabannin hukumar Alhazai ta Jihar Filato, ya bayyana haka ne a yayin da yake ganawa da manema labarai a Jos, albarkacin bikin cika shekaru 65 da samun ýancin kan Nijeriya, inda ya bayyana cewa, yawan danganta ýan ƙabilar Ibo da yaƙin basasa da ake yi a matsayin hujja don hana su zama shugaban ƙasa, ba adalci ba ne. “Tunda dai an sanya hannu kan yarjejeniyar yafiya ga kowanne ɓangare, bayan kammala yaƙin Biyafira, bai kamata a cigaba da tauye musu haƙƙoƙin su na ýan ƙasa ba,” in ji Alhaji Aminu.

Ya ƙara da cewa, kamar yadda tun a baya a cikin tsarinta Jam’iyyar PDP ta amince da tsarin karɓa-karɓa to, yana da kyau a wannan karon jam’iyyar ta duba yiwuwar mayar da mulkin Nijeriya ga yankin Kudu maso Gabashin ƙasar nan, waɗanda ba su taɓa hawa wannan kujera ba tun bayan samun ýancin kan Nijeriya.

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP a Jos ta Arewa, ya ƙara nuni da cewa, siyasar ƙasar nan ba za ta inganta ba, sai an bai wa kowanne ɗan ƙasa dama da ýancin ba da gudunmawar sa, musamman a manyan muƙaman siyasa, wanda akasari manyan ƙabilun ƙasar nan ke mamayewa, inda ya ƙarfafa buƙatar a kula da irin rawar ganin da ƙananan ƙabilun ƙasar nan ke takawa a lokacin zaɓuka, su ma a riƙa damawa da su.

Da ya juya kan shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2027 da ke daɗa gabatowa, jigon jam’iyyar PDP ya ja hankalin ýan Nijeriya, musamman matasa da shekarunsu suka kai na yin zaɓe a wannan karon su tabbatar sun yi rijistar katin su na zaɓe, a yayin da Hukumar Zaɓe ta INEC ta ba da dama, don sabunta katin zaɓe da gyare-gyare ga duk ýan Nijeriya. Domin su ma su samu damar zaɓen ɗan takarar da suke so ya jagorance su.

By ukarofi