Daga HABU ƊAN SARKI a Jos
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ƙara jaddada aniyarsa ta haɗa kan ‘yan Nijeriya tare da tabbatar wa mabiya addinin Kirista, musamman na Arewacin ƙasar nan, cewa gwamnatinsa a shirye take ta tabbatar da adalci ga dukkan addinai a cikin ƙasar nan.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da wasu shugabannin addinin Kirista a hedkwatar majami’ar COCIN dake Jos, a Jihar Filato.
Ya ce, “Ina da ƙudurin ganin na haɗa kan ƙasar nan da tabbatar da ci gabanta, kuma muna samun nasara akan haka.”
Da yake miƙa sakon ta’aziyyar sa game da rasuwar mahaifiyar shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Mama Lydia Yilwatda, wadda ta rasu tana da shekaru 83, Shugaba Tinubu ya ce, “A cikin iyalina muna da dogon tarihi na Musulunci, amma na auri Kirista, wacce take limamiyar coci, kuma ban taɓa tilasta mata canza addininta ba.”
Shugaban ƙasar ya shawarci shugabannin addini su tabbatar da goyon bayansu ga gwamnatinsa, tare da jaddada cewa, “A matsayinmu na shugabanni, ya wajaba mu gudanar da al’amuran addini ta yadda al’umma gaba ɗaya za ta amfana.”
Shugaban Tinubu ya kuma ƙara da cewa, Gwamnatin Tarayya tana aiki tuƙuru wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro, musamman a yaƙin da take yi da ‘yan ta’adda da masu garkuwa da jama’a.
“Muna samun galaba ga ‘yan ta’adda, kuma za mu cigaba da yaƙar su. Za kuma mu magance rikicin makiyaya da manoma,” cewar Shugaban ƙasa.
Shugaba Tinubu ya ce gwamnatin sa na ƙoƙari wajen ganin ta farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa, domin amfanin kowa da kowa.
A wajen jana’izar, Shugaban Ƙasa ya bayyana marigayiya Mama Lydia Yilwatda a matsayin uwa tagari mai jajircewa.
“Tarihin wannan coci yana da tsohon tarihi na ban gaskiya da riƙo da al’ada. Na taɓa zuwa Jos a baya, Gwamna Caleb Muftwang ya nuna min gidan Jakada Yahaya Kwande, inda muka taɓa taruwa a zamanin SDP, don tattauna makomar Abiola.
“A yau, ina godiya ga Allah da na ga wannan rana na zama shugaban ƙasa da na samu damar halartar jana’izar uwar al’umma mai sadaukarwa,” in ji Shugaban ƙasa.
Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nantawe Yilwatda, wanda shi ne babban mai karɓar ta’aziyya ya ce, mahaifiyarsa mace ce mai jajircewa wadda ta rayu ta na shan magani tsawon shekaru 47.
“Na zo in gode wa Allah bisa rayuwarta. Mahaifiyata ta yi aiki ba dare ba rana duk da yanayin lafiyarta, tana tallafa mana da ayyukan jinƙai,” in ji shi.
Ya gode wa Shugaban ƙasa Tinubu bisa kyautatawarsa tare da tabbatar masa da biyayyar sa da goyon bayan sa gare shi.
Shugaban Majami’ar COCIN, Rabaran Dakta Amos Mohzo, ya gode wa Shugaba Tinubu bisa tallafa wa Kiristocin Arewa, musamman wajen naɗa wasu a muhimman muƙamai, irinsu Sanata George Akume a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya da Farfesa Nantawe Yilwatda a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC da sauran su.
Shugaban Majami’ar ya kuma ƙara da godiya ga matakin Shugaban ƙasa wajen ba da gudunmawa ga inganta tsaro a jihohin Filato da Binuwai, tare da roƙon Shugaban ƙasa ya taimakawa waɗanda suka gudu suka bar gidajen su sakamakon rikicin Boko Haram daga wasu yankunan Borno da Adamawa, yayin da yanzu haka wasu da dama ke zaune ƙasar Kamaru.
Rabaran Mohzo ya tabbatar da cewa za su ba Shugaban ƙasa goyon baya wajen ganin ya cika alƙawuran da ya ɗauka na sabuntawa da samar da cigaban ƙasar nan.
Taron jana’izar ya samu halartar Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio; Shugaban Majalisar Gwamnonin Nijeriya, AbdulRazaq Abdulrahman; Gwamnonin APC; NSA Malam Nuhu Ribadu; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila; Ministan matasa, Ayodele Olawande, da sauran ministoci da manyan jami’an gwamnati.
Harwayau akwai, Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, da wanda ya riƙe wannan mukamin a baya, Boss Mustapha; tsofaffin gwamnonin Nasarawa, Bauchi, Filato, Kogi da Imo, da mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa na Jam’iyyar APC, Sanatoci, ‘yan majalisar wakilai, da wasu tsofaffin shugabannin majalisar wakilai da daraktoci daga ma’aikatar jinƙai ta tarayya.
