Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya, ta yi bikin cika shekaru 63 da kafuwa, sai dai Shugaban Jami’ar, Adamu Ahmed, ya ce jami’ar a cikin waɗannan shekaru ta rasa ƙwararrun ma’aikatanta waɗanda suka tafi saboda wasu damarmaki a cikin ƙasar nan da ma a ƙasashen ƙetare.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya rawaito cewa shugaban jami’ar ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da manema labarai a wani ɓangare na bikin cika shekaru 63 da kafuwa.
Ya kuma koka da cewa; “ma’aikata na rasa ƙarfin guiwarsu saboda cigaba da lalacewar gine-gine da rashin albashi mai kyau. Abin takaici ne yadda jami’ar ta rasa ma’aikata kusan 2,000 a cikin shekaru biyar ɗin da suka gabata.”
A cewarsa jami’ar na buƙatar ɗaukar ma’aikata da za su maye gurbin waɗanda suka tafi da kuma ƙarfafa binciken da ayyukan koyarwa.
“A yanzu akwai kwasa-kwasan da ake yi waɗanda kaso 95 na malaman da ke koyar da su farfesoshi ne.”
“Wannan abu ne da zai iya jawo rashin samun tantancewar kwasa-kwasans a nan gaba kaɗan da zai iya jawo ƙarancin malaman da za su maye gurbin waɗancan manyan malaman da ake da su,” ya bayyana.
Shugaban Jami’ar ya ce ƙarancin kuɗi kuɗi shi ma wata matsala ce da ke damun jami’ar wanda ya jawo rashin samun sabunta gine-ginen da samar da kayan abin karatu a ga laburare da tallafin gudanar da bincike.
Ahmed, ya ce, jami’ar na da shirin ganin ta mai da hankali wajen sabuwar hanyar koyarwa da za ta ƙunshi amfani da fasaha da tafi da ma’aikatanta domin samar da sakamakon da ake buƙata.
“Za mu ƙarfafa cibiyar karatu daga (DLC), wacce ita ce mafi girma a Nijeriya domin tabbatar da ilimi ya kai ga kowa a cikin gidansa da ba wa kowa dama.”
“Ta wannan hanya ce ABU ba kaɗai za ta ba da gudunmowa ba ne ga cimma manufofin samar da cigaba mai ɗorewa ba (SDGs), har ma da tabbatar da kowa ya samu ilimi da rage rashin daidaito da ake fama da shi” ya faɗa.
Shugaban jami’ar ya ƙalubalanci ƙungiyar tsofaffin ɗaliban jami’ar na rashin ba da gudunmowa ga jami’ar da ta tallafe su ta hanyar tallafa mata da ba da tallafi domin inganta gobenta.
Ahmed ya kuma yaba wa irin ƙoƙarin da gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ke yi ta hanyar tsare-tsare a fannoni daban-daban da ɓangaren ilimi.
