BIVAS da IReV ba za su iya magance matsalolin zaɓe a Nijeriya ba – Tsohon Shugaban INEC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu da ya sauka a kujerar kwanan nan, ya ce duk da cewa an ƙirƙiro amfani da na’urorin zamani don inganta harkokin zaɓe musamman wajen tabbatar da gaskiya da adalci a tsawon shekaru goma baya, hakan bai wadatar ba wajen hana samuwar matsaloli a lamuran zaɓen ƙasar.

Farfesan ya bayyana haka ne a wani sabon littafinsa mai shafi 200 da INEC ta fitar mai suna ‘Election Management in Nigeria: 2015-2025’, wanda ya yi tsokaci akan ayyukan INEC, nasarori, ƙirƙire-ƙirƙire da kuma ƙalubale a yayin zangonsa biyu a matsayin shugaban hukumar.

A ƙarƙashin jagorancinsa ne aka ƙirƙiri amfani da na’urorin tantancewa na BIVAS da IVED da kuma shafin IReV domin wallafa sakamako kai-tsaye ta yanar gizo da kuma ƙara adadin wuraren kaɗa kuri’a.

Littafin ya kuma yi tsokaci akan yunƙurin da ake yi wajen mayar da hanyoyin gudanar da zaɓuka cikin sauƙi, inda ya ce INEC ta shirya aiwatar da tsare-tsaren damawa da mata, matasa, nakasassu da waɗanda aka raba da muhallansu.

Saidai, a cewar Farfesan duk da waɗannan nasarori da cigabada aka samu a fannin, akwai ƙalubale da dama da ke zama alaƙaƙai a lamuran zaɓukan Nijeriya saboda hatta ababen fasahar da ake ganin sun inganta al’amuran, a wasu lokuta ba sa iya magance wasu matsaloli.

Ya bayyana cewa, a ƙoƙarin INEC na magance matsalolin, ta samar da tsare-tsaren wayar da kan al’umma, inganta lamuran jami’an zaɓe da haɗin-gwiwa mai ƙarfi da hukumomin tsaro domin bada kariya ga masu zaɓe kayayyakin zaɓe.

By Babaji