Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban majalisar Dattijai, Alhaji Abdul’aziz Maituraka ya faɗi haka a Katsina a wajen bikin karramashi bayan da gwamna Dikko Raɗɗa da ya bashi muƙamin babban mataimaki na musamman kan faɗakarwa.
Ya ce a iya sanin sa jihar Katsina babu wata jam’iyyar da za ta ja da gwamnatin APC ta Dikko Raɗɗa.
Maituraka ya godewa Mallam Dikko Raɗɗa bisa wannan nauyi da ya ɗora masa inda ya tabbatar masa da cewa zai tunkari yiwa APC aiki bisa amana da jajircewa.
Yayi alƙawarin zama da masu ƙananan sana’o’i a Katsina da suka haɗa da masu tuyan ƙosai, ƙuli da sauran domin duba hanyar da zai tallafa masu.
Sabon babban mataimaki na musamman wanda babban amini ne ga tsohon gwamna Aminu Bello Masari,ya ce iya sanin sa duk wanda ke tare da Masari ya na tare da Dikko Raɗɗa.
Mayan mutane da dama suka yi bayani kan Maituraka bisa kyautatawa da taimakon da yake yiwa al’ummar Katsina.
Ƙungiyoyin Mata da masu kiwon kaji da kifi , ƙungiyar matasa na ƙaramar hukumar Ɓatagarawa, ƙungiyar zawarawa da gidauniyar gwagware da sauran wasu ƙungiyoyi ƙarƙashin gidauniyar maituraka suka shirya taron karramawa ga shi Abdul’aziz Maituraka.
