Ministar Tinubu ta tallafa wa mata da matasa sama da 1000 a Nasarawa

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafia

Ministar harkokin mata ta Tarayyar Najeriya, Hajiya Imaan Sulaiman Ibrahim, a ƙarshen mako mako da ake ciki ta bayar da kayayyaki masu darajar miliyoyin nairori domin taimakawa sama da mata 1000 a ƙananan hukumomi 13 na Jihar Nasarawa a matsayin wani ɓangare na ayyukanta na jin ƙai ga marasa galihu a cikin al’umma.

A yayin wannan taro, ministar ta kuma ƙaddamar da shirin lafiya na musamman domin magance matsalolin lafiya a matakin ƙananan hukumomi a cikin jihar.

Kayayyakin da aka raba sun haɗa da: injin niƙa, kwalayen iskar gas na girki, injin ɗinki, turamen atamfofi, buhunan shinkafa, da injin tura ruwa, tare da tallafin tsabar kuɗi ga masu buƙata.

A wajen rabon kayayyakin a ƙaramar hukumar Keffi ta Jihar Nasarawa, Ministar ta bayyana cewa wannan taimako wani ɓangare ne na “Renewed Hope Agenda” na shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda manufarsa ita ce mayar da fata da goyon baya ga marasa galihu a cikin al’umma.

A cewar Hajiya Imaan, “Muna murnar shekaru na shirin sabon fata na shugaban ƙasa don mata, yara da iyalai. Kun sani, shekara guda kenan da aka ba ni wannan amanar, kuma abin murna ne saboda mun samu ci gaba wajen sake fasalin manufofi, ƙarfafa mata, yara, da iyalai.

“Yau muna murnar ci gaban wannan shiri na sabon fata, kuma na yi farin ciki ganin ku duka a nan wato daga jam’iyya, gwamnati, har zuwa masu cin gajiyar wannan shiri.

“Fiye da mutum 1000 ne suka amfana yau, daga gas ɗin girki mai tsafta, zuwa hasken rana, zuwa tallafin sana’o’in dogaro da kai, har da tallafin kuɗi ga ‘yan kasuwa ƙanana,” in ji ta.

Ta kuma bayyana cewa ma’aikatarta tana yin ayyuka a fannoni daban-daban, inda ta ce wannan lokaci ba shiri ne kawai ba, amma manufofi ne da suka zama aikace-aikace na zahiri kamar shirin lafiya, gas mai tsafta, tallafin gidaje, da ƙarfafa tattalin arzikin mata.

Hajiya Imaan ta ƙara da cewa shugaban ƙasa yana ɗaukar batun ƙarfafa tattalin arzikin mata a matsayin fifiko, wanda hakan ke sanya mata, yara da iyalai a tsakiyar ci gaban ƙasa.

Ministar ta kuma bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da shirin “Costed Action Plan” a turance na kawo ƙarshen cin zarafin yara, tare da jaddada cewa duk waɗannan shirye-shiryen an tsara su ne don amfanin jama’a a ƙasa.

Ta yi kira ga mata a jihar Nasarawa da su ci gaba da marawa gwamnatin APC baya, domin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana da kyakkyawan shiri ga ‘yan Najeriya.

A nasa jawabin, Ministan Harkokin Ayyuka na Jihohi, Mista Bello Goronyo, ya yabawa Ministan Harkokin Mata bisa wannan kyakkyawan aiki na mayar da alheri ga al’umma, wanda ya ce ya nuna amfanin dimokuraɗiyya.

Ya ce, “Wannan aiki abin yabo ne. Ina yaba ma ta ƙwarai da gaske saboda dawowarta cikin al’umma ta nuna tasiri sosai.

“Na ga kayayyaki da dama irin su injin ɗinki, zani, da sauran abubuwa da yawa da za a bai wa al’umma a matsayin mayar da alheri ga jama’a.

“Na san Imaan mace ce da jama’arta ke ƙauna, ita ma tana ƙaunar jama’arta. Ta nuna hakan a fannoni daban-daban, tana son ta taimaka, shi ya sa ake ƙaunarta,” in ji shi.

Mista Bello ya yi kira ga waɗanda suka amfana da kuma waɗanda ba su amfana ba su haɗu wajen mara wa shugaban ƙasa baya domin samun nasarar mulkinsa har bayan shekara ta 2027.

Haka kuma, a yayin taron, Shugaban Jam’iyyar APC na jihar Nasarawa, Dakta Aliyu Bello, ya yaba wa ministar bisa wannan shiri nata, yana cewa wannan tallafi zai kara inganta rayuwar masu cin gajiyar sa.

Dakta Aliyu Bello ya ce taimakawa mata da matasa zai taimaka sosai wajen rage wahalhalun jama’a a fadin jihar. To

By ukarofi