A idonmu aka yi komai, mu ma mun taya daidai gwargwadon ikonmu

Spread the love

Daga MUHAMMAD SANI YUNUSA AL-KANAWIY

Abduljabbar Kabara ya fara da’awarsa a bisa ƙoƙarin saɓa wa duk wani abu da abokan hamayyarsa suke yarda da shi, hakan ta sa, ya saɓa wa usul ɗin mazhabin da ya ke a kai ya gada daga iyayensa, misali, yarda da sahabban ma’aiki gabaɗaya, a bisa jagorancin Sa’adat, Abubakar da Umar da Usman da Aliyu, a jere, kawai don ’yan Izala suna ƙarfafa hakan!

Sai ya fara lalube da neman duk wata shubuha da za ta sanya ya zargi wani sahabi, don ya saba da yan Izala, waɗanda suna tsananin kiyaye wannan fage, kamar yadda saɓaninsa da yayansa khalifan gidansu, ya sa, ya yi ta ƙoƙarin soke abubuwan da Khalifa ƙaribu ya riƙe su gam, kamar anfasu da su mi’adi da bandiri da sauransu, ɗori akan aƙidar girmama sahabbai da aƙidar mahaifinsa ce, ya yi ta kushe abin da mahaifinsa ya gadar, kawai don ba ya shiri da wanda ya riƙe su gam.

Ahsunnah, musamman waɗanda yake kira da Izala, sun riƙe Bukhari da Muslim gam, to yana son ya saɓa da su, duk da yawanci aƙidar mahaifin nasa, da waɗannan littafai yake hujja, sai ya tasar ma yaƙar waɗannan littafai, sai ya tafi wajen Mustashrikai, masu amfani da Musulunci don rushe Musuluncin, ya ɗebo muggan fassarori da suke wa hadisan Ma’aiki (SAW) da wasu ayoyin Alƙur’ani, amma shi dai, ya dakata akan hadisan, yana ƙarfafar abin da suke yi, da sunan raddi, domin kawai a rushe littafan da wadanda yake gaba da su, suka riƙe gam!

Malaman Musulunci na gabaninsa, sun yi raddi, sun kawo fassarar ta gaske mai ma’ana, ba sharri ba, hakan a zamanin nasa, daga gidansu ma, an yi masa raddi, daga Tijjaniya daga Izala, an fi shekara ana masa raddi, a ƙure shi, hujja ta bayyana a gare shi, ya ƙi karɓa, ya guje wa zaman da ake nema a yi da shi, sannan ya doge a bisa yada wadannan munanan aƙidu, ba a iya audio ba, har littafai ya wallafa!

A wannan hali ne, ya ƙirƙiro wasu munanan lafuzza, wadanda babu su, ya jingina wa ma’aiki sallalLahu alaihi wasallama, ya nuna wadannan littafan ne suka zo da su, a wani salo na rashin lura da girman ƙadarin annabi Muhammad sallalLahu alaihi wasallama, aka nemi zama da shi, ya ƙi yarda, aka masa raddi, ya ƙi karɓa ya gyara, to shi ne aka nemi lallai gwamnati ta shigo, ba kuma wai ta hukunta shi ba, a’a, ta sa shi a dole ya zauna a yi mukabalar, kuma hakan aka yi a liɓe, aka ƙure shi, ya kasa nuna hujja ko daya, ya tuba ya ce ya janye, daga baya ya sake komawa kan da’awarsa!

Daga nan dai, gwamnati ta yi ƙararsa, Alƙalai sun ba shi sama da shekara, ya kasa tabbatar da da’awarsa, hatta littafan da yake kushewa din, Alƙali ya nemi ya nuna wajen, ya ce ba shi da su, aka yi masa gata, aka siyo masa, amma bai nuna ba, kuma bai karbi kuskurensa ba, ya doge, ya yi ta rigima da lauyoyinsa!

Duk mai ganin Mallam Lawan Triumph, irin abin da Abduljabbar ya yi, shi ma ya yi, to adalci, a bi matakan da aka bi akan Abduljabbar akan Malam Lawan, idan shi ma ya kasa, sai a yi masa ta Abduljabbar, amma ba molonka da zallar kiyayya ko siyasa ko son dole tun da an yi wa nawa, kai ma sai an yi wa naka!

Allah Ya ƙara mana son ma’aiki Ya hana mu riƙarsa, KARAN BARA, IƙAMATU ƙADHI!

Muhammad Al-kanawiy ya wallafa ne a shafin sada zumunta na intanet

By ukarofi