Daga ALI ABUBAKAR SADIK
Na haura shekaru hamsin a duniya wadda gaba dayanta a cikin nazari da karatun addinin musulunci ta wanzu har zuwa yanzu. Na fara karatun Allo a gidanmu, na je makarantar Malam Manzo Arzai, na kuma halarci makarantar buzu ta Marigayi Malam Auwalu Jazallah. A jami’a na karanci Islamic Studies inda na koyi tarbiyar research.
A duk tsawon wannan lokaci, duk da gidanmu yan Darika ne, ban taba wazifa ba, ban taba Mandiri ba, don haka ni tsawon rayuwata tun kafin na yi karatu mai zurfi kungiyar addini bata taba bani sha’awar bin kowacce iri ba. Amma sakamakon an bude tunaninmu na tambayar hujja a kan komai tun kafin muje jami’a, ta hannun yayanmu, Dr Abdullahi Bature, Allah ya ji kansa, wanda shi babban Dan Izala ne, da Malam Nasidi Goron Dutse, shi kuma Dan Tijjaniyya, a lokacin da mu ke tasowa tare da su a matsayin yayyenmu, mun kasance duk abinda wani zai fada, a kan addini ko rayuwa, to muna da slogan cewa “Me ye hujja?”. Kasancewar wadannan yayye namu na bangarorin akida daban daban, ya sa mun koyi girmama sabani da dogaro da hujja. Sannan kasancewar a secondary school mun karanci science, kuma Dr Ahmad Sarari, wanda a shekarar 1986 da mu ka yi GCE ya sami distinction 9, ya kasance group din mu na nazari muna shaukin science da neman hujja ta zahiri a kan abubuwa.
Wannan yasa jami’a ta kara tsefe tunaninmu wajen nazari da bincike. Na bazama nazarin dukkan kungiyoyin addinin musulunci, har Shia a wancan lokacin da ba’a bari ma ka karanta ta, na mallaki Tafsir Al-Mizan. Ba ma Shia ba, har Ahmadiyya sai da na nemo mujalladan Tafsir Al Kabir na Bashir Ahmad, wato Dan Ahmad Gulam wanda ya kawo darikar Ahmadiyya. Bayan nan, sakamakon bibiya da nazarin Ahmad Deedat, wanda ya kawo mana nazarce nazarce a kan kiristanci, ya sa na mallaki Bible wanda har gobe abokin nazari na ne. Sannan kuma ta dalilin Deedat din muka fara nazarin babban Malamin yan ƙurani zalla na Duniya, wato Rashad Khalifa, wanda yayi da’awar manzanci. Na karanci duk rubuce rubucensa da kallar biliyoyin sa har na mallaki Tafsirin sa na ƙurani da Turanci, The Last Testament. Bangaren Sunna kuwa, tun kafin na je jami’a na karanci Sahihul Bukhari da Muslim, wadanda su ne tafarkin shiriya na farko da ya kaini ga nazarin tafsirin ƙurani. A takaice babu wata kungiya ta addinin musulunci da ban yi nazarinta daidai gwargwado ba.
Babban darasin da na koya a duk kungiyoyin addinin musulunci shine cewa babu wata wadda akwai sashen da ba ta dara saura a kan da’awarta zuwa ga gaskiya ba, amma kuma kowacce ta na da na ta kuskure. Abubuwa biyu ne su ka hana ni shiga kowacce irin kungiya
1. A karance karance na na tarihi, na fuskanci cewa a shekaru akalla 30 na farko bayan Hijra, wato zuwa lokacin sayyidna Ali, babu wani abu wai shi kungiya a musulunci. Wato duk da cewa kawunan musulmi sun fara rabuwa daga ranar da Annabi ya yi wafati, banbancin ya tsaya ne ga siyasar mulki ba ta addini ba. To don haka a mahanga ta, idan ma so kake ka koma kan Salaf, to babu wadanda su ka kai Khulafa-ur-rashidun, kuma dukkansu babu wanda yayi kungiya kowacce iri. Tushen rarrabuwarmu ya faro daga shi’anci, sunna da kharijanci dalilin siyasar halifanci, kuma shine annobar da ke bibiyar mu har yanzu da ya juye kan akida.
2. Hadisin da ke cewa musulmi zasu karkasu kungiyoyi 73, kuma cikinsu guda daya ce za ta samu tsira. Na tambayi kaina to wacece wannan? Dalili na na cewar Khulafa-ur-rashidun ba su yi wata kungiya ba, ya jaddada mun cewa to lallai na kaucewa kowacce irin kungiya. Domin a Salaf ba wanda ya cancanci na kwaikwaya irinsu.
3. Hujja ta uku, kuma mafi girma ita ce ayoyi biyu a cikin ƙurani ƙ6:159 “Lalle ne waɗanda suka rarraba addininsu, kuma suka kasance ƙungiyã-ƙungiyã, kai ba ka zama daga gare su ba, a cikin kõme: abin sani kawai al’amarinsu zuwa ga Allah yake. Sa’an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka kasance sunã aikatãwa.”
Idan Allah ya gargadi Annabi kansa cewa ba shi da wata alaka da duk wani wanda ya rarraba addini zuwa kungiya-kungiya, to don me ni zan bi wata kungiya? Sannan ya sake ce mana; ƙ3:105 “Kuma kada (musulmi) ku kasance kamar waɗanda suka rarrabu (kungiya-kungiya) kuma suka sãɓã wa jũna, bãyan hujjõji bayyanannu (littafi) sun je musu kuma waɗannan sunã da azãba mai girma.”
Wadannan dalilai sun gamsar da ni da irin abinda ake cewa a kotun Shari’a “Beyond reasonable doubt” cewar wajibi ne na guji duk wata kungiya. Shi yasa hatta shi wannan Sectless ba na son a kira ni da shi, domin tun da na taso bani da wata kungiya da na jingina da ita, don me zan fara a yau?. Ni dai musulmi ne, wanda ya yarda da koyarwar ƙurani a matakin farko a kan komai, kuma na yarda da duk wani hadisi da bai ci karo da ƙurani, tarihi ko kimiyya ba. Haka kuma na yarda da duk wani Ilimi mai amfani wanda hankali ya gaskata shi. A karshe ina kokarin kasancewa cikin wadanda Allah, kafin ya kawo waccan ayar ta gargadin kada musulmi ya yi kungiya, ya bada umarnin cewa kowa kawai ya yi kokarin zama… ƙ3:104 “Kuma wata jama’a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alhẽri, kuma suna umurni da alhẽri, kuma suna hani daga abin da ake ƙi. Kuma waɗannan, sũ ne mãsu cin nasara.”
Ni, wannan ya ishe ni, kuma Allah da kansa ne ya assasa mana cewa; ƙ3:64 “Ka ce:.. kada mu bauta wa kõwa fã ce Allah. Kuma kada mu haɗa kõme da Shi, kuma kada sãshenmu ya riƙi sãshe Ubangiji, baicin Allah.” To, idan sun jũya bã ya sai ku ce: “ku yi shaida cẽwa, lalle ne mu musulmi ne (kawai).”
To, bi musulmi ne, na yi bara’a da kowacce irin kungiya, kuma duk wanda ke son nasara ya yi watsi da kungiyanci kowane iri, ya maida hankali wajen ganin cewa duk umarnin alheri da Allah ya yi a ƙurani, ya dabbaka shi, sannan ya goyi bayan hani ga duk wani abin ki. Wannan ce hanyar tsira, wannan shine musulunci, kuma ita kadai ce hanyar da zata hade musulmi waje guda yadda karfinmu zai bayyana sannan nasararmu ta tabbata. Idan mun ki kuma, to tabbas za mu ci gaba da rayuwa cikin wannan rauni da mu ka kirkirawa kan mu na bangaranci da kungiyanci tun asali. A karshe dai kuma kowa zai girbe abinda ya aikata ne, ba wanda zai dakon aikin wani.
Allah ya ganar da mu baki daya.
Malam Ali manazarci ne a Kano
