Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
A ƙoƙarin magance rikici da tabbatar da zaman lafiya, kwamitin shura na Jihar Kano ya gana da Malam Lawal Abubakar, da aka fi sani da Triumph, a ofishin hukumar tsaro ta DSS. Ganawar na da nasaba da zarge-zargen da ake masa na yin wasu kalamai da ake ganin sun ƙunshi ɓatanci ga Manzon Allah (SAW).
Wannan mataki ya biyo bayan ƙarar da wasu malamai da al’ummar Musulmi suka shigar, inda suka buƙaci a ɗauki matakin doka akan kalaman da Malam ya yi a cikin wata huɗuba ko wa’azi da ya gabatar.
Kazalika, kwamitin ya bayyana muhimmancin bin dokoki da tsare martabar addini, tare da jaddada cewa ba za su lamunci duk wani abu da zai tayar da hankali ko tunzura jama’a ba. Sun kuma buƙaci al’umma da su zauna lafiya yayin da hukumomi ke ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Ana dai sa ran za a fitar da bayani dalla-dalla daga hukumomin tsaro bayan kammala binciken da ake yi. Al’umma kuma na fatan a ɗauki matakin da ya dace, cikin adalci da gaskiya.
