
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban ƙungiyar jagororin matasan Arewa ta NNYLF, Kwamared Murtala Muhammed Gamji tare da sauran membobin ƙungiyar, sun yi gargaɗi da kuma bayyana rashin goyon bayansu ga yunƙurin neman a sako shugaban ƴan fafatukar kafa ƙasar Biafara, Nmadi Kanu daga wasu jagororin al’umma Nijeriya.
A cewar Kwamared Gamji, tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma jigo a jam’iyyar adawa, Alhaji Atiku Abubakar da ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore ne suke shirya zanga-zangar neman sako jagoran Biafaran.
Ƙungiyar matasan ta kuma yi watsi da masu kiran a sake shugaban ƴan tawaren na IPOB, Nnamdi Kanu.
A yayin ganawa da manema labarai, shugaban ƙungiyar Kwamred Murtala Gamji ya yi alla-wadai da shaharerren ɗan gwagwarmaya Omoyele Sowere kan shirin gangamin neman sake Kanu.
Kwamared Gamji ya zayyano ƙasashen da kashe-kashe da ake alaƙantawa da IPOB da dirar mikiya kan ‘yan Arewa.
Ya kuma bayyana shirinsu na yin gangamin nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu na kwanaki uku bisa gyare-gyaren da gwamnatinsa ke yi, wanda za su fara a ranar 20 ga watan Oktoba, 2025.
