
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar kula da Gidajen Gyaran Hali ta Ƙasa (NCoS) reshen Jihar Kano, ta ce ta mayar da fursuna, Sheikh Abduljabbar Kabara gidan yarin da ke ƙarƙashin ikon tarayya ne saboda la’akari da tsare-tsarenta na gudanarwa.
Jami’in hulɗa da jama’arta, CSC Musbahu Lawan Ƙofar Nassarawa ya faɗi haka a wata takarda, ranar Laraba.
Ya bayyana cewa, sauya wa fursuna sheƙa daga wannan kurkukun zuwa wani ya danganta ne da matakin tsaro a wajen da aka ajiye shi, wanda kuma hakan yana ƙarƙashin dokokin hukumar gyaran 2019, kamar yadda ya shar’anta.
Ya kuma ce, akan ɗauki irin matakin idan an yi la’akari da tsaro, irin fursuna, samuwar wasu gidajen yari da buƙatar gyaran hali.
CSC Lawan ya tabbatar da cewa ana bada cikakkiyar kariya ga walwala da ƴancin shari’a na Malam Abduljabbar kamar yadda doka ta tanada.
A ranar 15 ga watan Disambar 2022 ne Babbar Kotun Shari’a da ke zaune a Kano ƙarƙashin Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola, ta yanke wa Abduljabbar hukuncin kisa ta hanyar rataya kan laifin ɓatanci.
